Gwamnonin Jam’iyyar PDP, a yau Litinin sun kalubalanci gwamnatin tarayya kan sakaci da wulakanta albarkatun mai da na gasa a kasar.
Gwamnonin sun bayyana cewa, shigar da kudade cikin asusun gwamnatin tarayya ya kasance cikin rikici, rudani, da rashin gaskiya, sun bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da zabe mai zuwa wajen kakkabe jam’iyyar APC.
A jawabin bayan taron gwamnonin PDP na yau wanda Shugaban Kungiyar Gwamnonin, Aminu Waziri Tambuwal ya karanta bayan kammala taron, an yi kira ga ‘yan majalissun Najeriya da su gaggauta kammala tattaunawa kan kudirin gyaran dokar zabe ta hanyar sanya tabbatar da dokar ko kuma su cire sassan da ake takaddama a kai.
Gwamnonin dai sun debe kimanin awanni hudu suna zaman wanda aka gudanar a babban birnin jihar Rivers, Port Harcourt.
Gwamnonin sun nuna rashin jin dadinsu game da maganganun shugaban kas ana kwanannan wanda sukai nuni da watsinsa game da ‘yan sandan jihohi, da kuma kin kulawarsa wajen yin abin da ya dace a magance matsalar tsaro a Najeriya, sun yi kira gare shi da ya yarda da tsarin bayar da damar kulawa da tsaro ga sassan kasa a matsayin hanyar magance matsalar tsaro, hadi da samar da wadatattun makamai, kudade da kuma horon da jami’an tsaro suke bukata.
Takardar bayan taron ta kuma kalubalanci gwamnatin tarayya kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar a hannunta, wadanda suka hada faduwar darajar naira, karuwar rashin aikin yi, da kuma yawan ciyo bashin da ba a amfani da shi yanda ya kamata, da kuma sauran abubuwan da suke nukusa tattalin arziki.
KU KARANTA: Hukumar Zabe Ta Sanya 26 Ga Fabarairu Domin Zabubbukan Maye Gurbi
Takardar ta ce, “a tsarinta, a bayyane yake cewa Gwamnatin APC asara ce idan aka kwatanta ta da abubuwan da PDP tai lokacin tana gwamnati. PDP ta mika mulki da tattalin arziki wanda yawansa ya haura dala biliyan 550, mafi girma a Afrika, amma a zamanin APC Najeriya ta zama cibiyar talauci ta duniya.
“A shekarar 2015, karkashin PDP, canjin naira zuwa dala yana naira 198 ga duk dala daya, yanzu kuma ta kusan naira 500 ga dala daya; a bangaren rashin aikin yi kuma, a lokacin PDP yana kaso 7.3 cikin 100, amma yanzu yana kaso 33 cikin 100 daya daga cikin mafi kamari a duniya; A shekarar 2015, kudin man fetur yana naira 87 kowacce lita, yanzu kuma yana naira 165 kowacce lita kuma yana kan karuwa karkashin kulawar APC. Biyan bashi a lokacin APC yana lakume sama da kaso 98 cikin 100 na kasafin kudi. Matsalolin sun fi karfin lissafawa.
Gwamnonin sun kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi rijista da hukumar zabe, INEC domin tabbatar da ‘yancinsu a babban zabe me zuwa na shekarar 2023.
Takardar bayan taron ta kuma ce, “zabe mai zuwa zabe ne mai matukar muhimmanci da za ai amfani da shi wajen kawo karshen danniyar APC twadda ba ta kishin matasa; gwamnatin da take da rashin tausayi wadda ta hana ‘yan Najeriya anfani da TWITTER, kafar sadarwar da take temakawa harkar kasuwancin matasa, na sama da shekara guda. Ya kamata matasa su sami kwarin guiwa, su yanke hukunci kan wanda suke so ya jagorancesu.
Gwamnonin da suka sami halartar zaman sun hada da: Tambuwal (Sokoto), Udom Emmanuel (Akwa-Ibom); Sen. Douye Diri (Bayelsa); Samuel Ortom (Benue); Dr. Ifeanyi Okowa (Delta); Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu); Engr. Oluseyi Abiodun Makinde (Oyo); Ahmadu Umaru Fintiri (Adamawa); Bala Mohammed (Bauchi) da gwamna mai masaukin baki, Nyesom Wike (Rivers).