Gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) za su zauna ranar Laraba a Abuja domin duba shawarwarin da kwamitin duba karba-karba a shirye-shiryen babban taron kasa na jam’iyyar da za a gudanar a ranakun 30 da 31 ga Oktoba.
A Litinin din nan, sanarwar gayyatar zaman ta zagaya tsakanin dukkanin gwamnonin wadanda ake sa ran su kasance a Abuja domin zaman.
Jaridar PUNCH ta rawaito a baya cewa, rahoton kwamitin da Gwamnan Delta, Ifeanyi Ugwanyi ke jagoranta ya mika kujerar jagorancin jam’iyyar zuwa yankin Kudu, yayin da kuma ya mika kujerar sakataren jam’iyyar zuwa yankin Arewa.
Wannan ya jawo cecekuce a yankin Kudu maso Gabas wadanda sukai tsammanin jam’iyyar za ta mika shugabancin zuwa Arewa domin a bude yankin Kudu damar samun dan takarar shugaban kasa.
Wani da ya bukaci a boye sunansa saboda rashin samun damar bayyana bayanan daga na sama da shi, ya ce; “Har yanzu ana kan tattaunawa kan batun.
“Duk abin da muka amince a kai bayan mun tattauna da gwamnoninmu a ranar Laraba za mu gabatar ga Kwamitin Gudanarwa na Kasa na jam’iyyar wanda za su gabatar ga Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar domin tabbatarwa.”