For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnonin PDP Za Su Yi Taro Yau, Za Su Mika Takarar Shugaban Kasa Zuwa Yankin Arewa

Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP za su gana a yau Litinin a birnin Port Harcourt domin duba shirye-shiryen da jam’iyyar ta yi na samun mulkin Najeriya a shekarar 2023.

Darakta Janar na Kungiyar Gwamnonin PDP, Cyril Maduabum ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi a wata sanarwa da ya saki mai taken ‘Gwamnonin PDP za su Gana a Port Harcourt kan Shirin Kubutar da kuma Gina Najeriya’.

Duk da cewa sanarwar ta Maduabum ba ta nuna cewa kungiyar za ta tattauna hanyoyin samun nasarar zaben 2023 ba, an gano cewa gwamnonin za su tattauna kan karba-karba tare da baiwa shugabancin jam’iyyar shawara kan inda dan takarar shugaban kasa ya kama ya fito.

Sai dai kuma, Daraktan Janar din ya ce a zaman za a tattauna kan “duba yanayin da jihohi suke ciki, yanayin da kasa take ciki da kuma shirin PDP na samar da shugabancin da ya dace domin kubutarwa da kuma sake gina Najeriya.”

A cikin sanarwar, Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ne zai jagoranci zaman na farko a wannan shekara.

Maduaban ya kara da cewa, an gaiyaci Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu domin ganawa da gwamnonin kan hanyoyin samun nasarar shirin kubutarwa da kuma sake gina Najeriyar.

“Gwamnonin PDP suna aiki tare da tuntubar sauran shugabannin jam’iyya, musamman shugabancin jam’iyyar karkashin shugaban jam’iyya na kasa, Ayu, domin fitar da ingantacciyar hanya da kuma shiri na sake gina ingantacciyar Najeriya.

Maduaban ya bayyana cewa, ana sa ran duk gwamnonin jam’iyyar zasu halarci zaman wanda Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers zai zama mai masaukin baki.

Wannan zama na gwamnonin PDP, na zuwa ne awanni 48 kafin muhimmin zaman da Kungiyar Gwamnonin Najeriya za tai wanda Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti zai jagoranta.

Wani makusancin daya daga cikin gwamnonin PDP ya ce, akwai yiwuwar gwamnonin PDP su tattauna kan batun karba-karba a takarar shugaban kasa.

Majiyar ta kuma kara da cewa, akwai yiwuwar gwamnonin PDP bayan zamansu na yau, za su shawarci shugabancin jam’iyyar ya mika takarar shugaban kasa zuwa yankin Arewa a matsayin shiri na dawowa kan karagar mulki a 2023.

Majiyar ta ce, “duk da dai jam’iyyar a baya ta ce, za ta bar damar tsayawa takara a bude ga dan kowanne banagare, amma dai damar ta fi karfi ga yankin Arewa domin a samu nasarar samun kuri’un ‘yan Arewa.

“Akwai masu son mulki a Arewa wadanda ba sa son hakura da mulkin, saboda haka, jam’iyyar PDP zai fi mata sauki ta mika tikitin takarar ga yankin Arewa tare da zabar ingantaccen mataimaki daga bangaren Kudu.

“Akwai ganawa da dama da a yanzu haka ake kan yi, kuma ina tabbatar muku cewa, jam’iyyar PDP za ta dace a wannan lokacin.

Lokacin da aka tuntubi, Maduabum kan batun karba-karbar ya ce, ba zai iya kara wani abu ba sama da abun da ya fada a sanarawar da ya sakiwa ‘yan jaridu.

Comments
Loading...