Kai kawo tsakanin masu mulki a wannan lokaci wajen gyaran dokar zabe gabanin kusantowar babban zabe na kasa a shekara mai kamawa, kan iya kawo babban kalubale game da kyakkyawan zaton da ake yiwa Shugaba Muhammadu Buhari na kara inganta mulkin dimokiradiyya, musammman ganin yadda yake da dangantaka da talakawa yan dangwale. Gyara dokar zabe ba kawai zai gyara inganta dimokaradiyya bane, zai ma kara daukaka darajar dimokaradiyyar Nijeriya ne a duniya.
Jayayya ko koma bayan da ake samu wajen aiwatar da wannan doka, yana sake nuna jayayya da rashin yarda tsakanin gwamnonin wannan kasa da yan majalissun tarayyar na wannan kasa. Wannan dalili ya sanya jan kafar shugaba Buhari wajen sanya wa dokar hannu, wanda daga baya, bayan ya yi shawarwari da hukumar zabe ta kasa da bangaren ofishin babban lauya na kasa ya maida wa majalissar kasa dokar da dalilan sa na kin sanya hannu a kan Dokar.
Dalilan da suka sanya Shugaba Buhari kin sanya hannu a kan dokar a baya sun hada da kudirin da yan majalissa suka kawo cikin dokar na tilastawa jama’iyyun siyasa gudanar da zaben fidda gwani wato primary election ta hanyar zaben kai tsaye ko yar tinke da ake kira da direct primaries, bisa dalilin cewa aiwatar da wannan zabe yana bukatar kudade masu yawa da ga jama’iyyu, wanda wannan zai iya shafar hatta tattalin arzikin kasa dadi da kari ga yanayin da ake ciki na rashin tsaro a kasa.
Duk da cewar masu nazartar harkokin siyasa, na ganin cewa kin sanya hannun Shugaba Buhari ya zo ne wajen kin amincewar gwamnoni game da dokar da kuma matsin lambar da gwamnoni da wasu ministocin ga Shugaba Buhari ne ya hana shi sanya hannu a kan dokar.
Majalissun dokoki na Kasa, sun bada kai bori ya hau game da gyaran dokar, suka sake sanya karin zabi guda biyu ta yadda jama’iyyu za su gudanar da zaben fidda gwani har ta hanya uku, yadda za su iya yin sasanto wato consensus, zaben delegates wato Indirect Primaries da kuma Direct Primaries. Kusan wannan tanadai sune Shugaba Buhari da ma Gwamnoni suka so.
Sai dai kuma ba annan gizo ke yin sakar ba, a dokar cikin sashe 84(9)(a) ya bayar da damar “ Jama’iyyar siyasa da tayi tsarin sasanto, dole sai dan takara ya samu rubutacciyar amincewar dukkanin yan takarar da suke neman wannan kujerar, sun bayyana amincewar su na janyewa daga takarar, sannan sun amince da takarar wadda suka yardewa”.
Sanann a sashe na (b) ya kara da cewa “idan har jama’iyya ta kasa samun rubutacciyar takardar yarjejeniyya da ga dukkanin yan takara, to jamaiyya za ta koma ta yi zaben na kai tsaye ko amfani da delegates wato indirect election wajen zaben wanda zai yi wa jama’iyya takara…”.
Har ila yau a sashe (c) ya kara da cewa “..dole sai an samu taro na musamman (special convention or nomination congress) wanda zai tabbatar da dantakarar da a ka fidda ta hanyar sasanto, a wuri na musammsan a matakin kasa, ko yankin senator, yankin danmajalissar tarayya ko Jaha……”.
Bayan wannan kudurai, ta sake cewa dole wanda yake rike da mukami wato Official Public Officers kuma yana son tsaya wa takara sai ya sauka da ga kan mukamin sa a Gwamnatin Tarayya ko kuma a Jaha kafin ayi zaben fidda gwani wato primary election.
Wata sabuwa, duk da kasancewar yan Majalissun Tarayya sun bada kai bori ya hau wajen gyaran wadannan dokoki, sai dai karin wannan kudururruka basu yiwa mutane da dama dadi ba, musamman ma gwamnoni wa yanda suke da karfi a wajen sanya wa jama’iyyu yan takara bisa karfin da suke da shi wajen mallakar wadannan jam’iyyu.
Wasu gwamnonin ma na ganin sanya wadannan kudurai kamar neman tauye musu fada ajin da suke da shi ne a cikin jamaiyyu, duk da su yan majalissa suna ganin yin hakan sake ba da dama ce ga yan jama’iyya wajen shiga a dama da su a harkar zabe, musamman gyaran da akayi na wajen fidda dan takara ta hanyar consensus.
Su kansu masu rike da mukamai, wannan gyaran bazai yi musu dadi ba, zaiyi mutakar wahala mai rike da babban mukami kamar ministoci ko manyan hukumomi na gwamnati su sauka daga mukaman su tun kafin a yi primary election, wanda bai zama lalle a sake nada su wannan mukaman ba koda sun fadi a zaben.
Shin fidda yan takara ta hanyar sasanto zai yi sauki kuwa? Ganin yanayin rigingimun da suke damun jama’iyyun Nijeriya bisa tabbacin amfani da wannan doka.
Har yanzu dai zamu iya cewa a kwai sauran rina a kaba, ganin cewa har yanzu ana jiran Shugaban Kasa ya rattabawa dokar hannu, duk da cewa akwai rade radin matsi ga shugaban kasar daga gwamnoni na ganin ya sake kin amincewa da wadannan gyararrakin. Amma ko ma menene lokaci kadai zai nuna.
Ahmad Ilallah
alhajilallah@gmail.com