For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Haɗin Kai Duk Da Bambance-Bambancen Dake Tsakaninmu

ƘUNSHIN BAYANAN DA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR AKWA IBOM, UDOM EMMANUEL YA GABATAR A WANI TARO MAI MUHIMMANCI DA YA GABATAR YAYIN WANI TARO DA GAMAYYAR ƘUNGIYAR KULA DA KAFOFIN YAƊA LABARAI DA CIGABAN AREWA SUKA GABATAR A GIDAN AREWA, KADUNA – 4 ga NUWAMBA, 2021

Bari na fara godewa shugabancin ƙungiyar kafafen yaɗa labarai, tuntuɓa da kuma cigaban arewa akan wannan yunƙurin nasu na samar  da zaman lafiya a Najeriya da kuma yunƙurin tabbatar da haɗin kai a ƙasar nan , a daidai lokacin da ƙabilancin yare da addini suke ƙoƙarin yaga ƙasar nan sai ga shi su kuma sun shirya yadda za’a samu haɗin kai.

Wannan hukuncin ya yi daidai kuma an yi shi a lokacin da ya dace don ganin an ci gaba da samun haɗin kai a ƙasar nan, domin rashin yin hakan kan iya kawo cikas ga ƙasar nan.

A yanayin halin da ake ciki a ƙasar nan yanzu, yanayin matsalar tsaron da muke ciki ta yi kama da lokacin yaƙi, wannan abun zai zaburar da mutane wajen samar da haɗin kai, zaman lafiya da kuma soyyayyar juna. Addu’ata shi ne Ubangiji ya sa wannan zama ya yi sanadiyyar ƙarin soyayya da kuma fitar ƙasar nan daga cikin duhun da take ciki zuwa wani sabon tafarki na haɗin kai da kuma zama yan’uwan juna ga mutanen ƙasar nan.

Tun 1995, yanayin soyayya da zaman lafiya ya samu tsaiko a Najeriya. Kuma babu wanda ya yi wani abun, kunzo da muhimmin abu wanda zai samar da cigaba a ƙasar nan kuma kuka gayyato mutane masu kima da daraja a cikin Najeriya domin su yi magana akan wannan matsalar.

Sama da ƙarni ɗaya, ƙasarmu ta tsinci kanta a cikin matsalolin da suka dinga kawowa haɗin kanta damuwa saboda bambancin dake tsakanin mutanan . da yawa daga ciki sun kawowa ƙasar nan cikas, amma duk da haka ƙasar nan ta cigaba da zama a matsayin abu ɗaya duk da dai akwai kalubale a cikin haɗin kanmu wanda ya ba mu cikas da yawa, amma rushinmu, da kuma yanayinmu a matsayin ƙasa yana nan akan haka duk ƴan Najeriya sun amince da hakan.

Mai girma kuma jajirtaccen jagora shugaban shiyyar arewa Sardaunan Sokoto, Ahmadu Bello ya taɓa yin wata magana akan wannan kalubulen cikin hikima da ƙwarewa inda ya ce “a nan arewacin Najeriya muna zaune da yaruka mabanbanta, addinai amma muna zaune haka, abun da ya haɗa mu ya fi wanda zai raba mu muhimmamci.”

Yayin bukin  ranar ƴancin kai na farko wanda akayi a ranar daya ga watan Oktoba 1960, gwani wajen iya magana, mutum mai daraja Abubakar Tafawa Ɓalewa ya faɗi wannan kalmar mai muhimmanci: “za mu kare haƙƙin junanmu, ina tabbatar da tarihi ba zai manta da mu ba har abada kuma yanzu ga shi mun ginu ginuwa ta kirki.”

Duk wata magana da ta fito daga zuciyar waɗannan mutanen daidai ne. Abun baƙin ciki shi ne duk wasu abubuwa da suka tsara domin tabbatar da su yanzu an watsar da su, maimakon a bunƙasa su, a tsara su bisa hanyoyi masu kyau waɗanda za su ƙarfafa zaman mu a matsayin ƙasa ɗaya, duk wasu bukatu ne suke kawo mana cikas shi ne ya sanya muke jifan junanmu da kalaman da ba su dace ba, musamman saboda kabilancin yare wanda su ne suka girma har suke kawo mana rabuwa tsakanin mutanen mu.

Su ke ƙoƙarin rusa ginin da yake da karfi, lokacin da muke ƙoƙarin karɓar ƴancin kai, tabbas hakan ya taimaka mana wajen ganin ƙasarmu ta zama ɗaya ba tare da samun wani cikas ba, akwai buƙatar mu sake nazartar waɗannan abubuwan tare da tabbatar da sun yi aiki yadda ya kamata domin kawo ƙarshen waɗannan matsalolin da suke damun mu a yau. Mu tabbatar da haɗin kan Najeriya, amma muna buƙatar mu haɗa ƙarfi da ƙarfe don tabbatar da hakan cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba.

A 1996, a Atlanta dake Amurka mun nunawa duniya cewa za mu iya yin komai idan muna da haɗin kai. Mun samu nasara kan ƙasar Barazil duk da sun ci mu 3 kuma mun ɓarar da bugun daga kai sai mai tsaron raga kuma sun fi mu ƙarfi a wasan. Ƙasa da minti ashirin a tashi daga wasan, mun yi nasara akansu da ci uku da ɗaya. Saboda haɗin kan da Najeriya take da shi babu wanda zai yi nasara akanmu duk da mun ɓarar da bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Mun yi nasara kuma mu ne ƙasa ta farko a yankin Afirka da ta yi nasarar lashe babban kofi a gasar Olympic. Mun yi nasara ne saboda mun shirya sosai; wannan shine abinda Sunday Oliseh, ɗan wasan tsakiyar ya ce, akan nasarar da muka yi “Ku yadda da ni, gaba ɗaya rayuwar da na yi ta ɗan wasan ƙwallon kafa. Ina ganin babu wani lokaci da muka shiryawa komai, ba mu da kayan aiki, ba mu da aiyukan raya ƙasa, kai ko da kayan kula da lafiya ba mu dashi …. Bamu da isasshen abinci, ba mu da komai, mun zama kamar marayu.”

Amma saboda zuciyar tana da kyau, saboda kowa ya yadda kowa ɗan uwan kowa ne, kuma kowa ya yadda ba’a  nasara sai da haɗin kai, wannan ya sa ƙungiyarmu ta yi nasara. Me ya sa wannan tawagar ta yi nasara? Ga amsa daga bakin ɗaya daga cikin ƴan wasan, Victor Ikpeba, Najeriya ƙasa ce da take cike da kabilanci, ba za mu ƙaryata haka ba…. amma idan mun shiga fili kowa yana ajiye ƙabilanci a gefe har sai mun dawo gida, muna zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, idan muka dunƙule babu wanda zai yi nasara akan mu.

Irin wannan haɗin kan ne ya ba mu nasarar samun ƴancin kai. Marigayi tsohon gwamna Solomon Lar ya faɗa mana akan yadda aka yi aka samu ƴancin kai a Najeriya, “mun yi aiki tare a matsayin masu kishin Najeriya ba tare da duba bambancin dake tsakaninmu ba domin tabbatar da buƙatarmu “- Mai girma Dr. Nnamdi Azikiwe yayin da yake bayani ga wata gamayyiyar kungiya ta haɗa manyan mutane mabambanta (NAACP) a filin Polo, birnin New York, Yuni 19, 1959. Ya ayyana cewa “Dukkan manyan shiyyoyin da muke da su suna da bambanci, dukkansu suna da bambancin yare da kuma yanayin muhalli amma duk da haka saboda yanayin siyasa muke zaune a matsayin ƙasa ɗaya sama da shekaru hamsin. Wannan ya sa muke ganin siyasa ce kaɗai za ta ba mu dauwamammen haɗin kai a matsayin Najeriya don haka haɗin kan siyasa ya zama dole”.

Wasu masana siyasa sun ce babu waɗanda suke yin nasara a mulkin dimukraɗiyya idan babu haɗin kai, sun bayar da hujja ne da bayar da misali da manyan ƙasashe irin su Japan, Germany kai harma da ƙasar Amurka hadin kai ne ya kai su inda suke da ba su haɗa kai ba ba za su yi nasara ba.

Don haka, Najeriya ƙasa ce wadda take cike da bambance-bambance amma Masu ban sha’awa, duk abubuwan da suka raba mu kuma su ne zasu haɗa mu. Yare ne, kabila ce, ko yanayin abinci ko addini? Mu ɗauka , misali yadda ake cin goro, da yawa ba su san a kudu maso yamma ake noman sa ba, ana amfani da shi yayin Addu’oi a gabas, kuma ana cinsa don nishadi a arewa. Abu ne mai tsawo a yankin Yarabawa da kuma yankin Ijaw da Hausa duk suna rayuwa a waje daya, misali albasar da muke amfani da ita tana zuwa ne daga Arewa ; ake sauke ta a Ofe Nsalla a kudu , da kuma Ewedu a kudu maso-gabas da kuma Afang a yankina dake Uyo.

Muna mantawa da bambancin Addininmu duk lokacin da wani babban kasuwanci ya taso, babu wanda yake cewa Ahmed yana ambaton Allah amma Adewale yana ambaton Hallelujah. Dukkansu murna muke a cikin banki.

Mu ne ƙasar da muka samar da dalar gyada a Kano. Inda ƙwararru daga Malaysia suka samar da man fetir a kudu-maso kudu da kuma kudu maso-gabas da kudin. Duk Najeriyar ɗaya ce da ta yanzu, yaren ɗaya ne, bambancin Addinin ma, kuma tarihin ɗaya ne, kuma yanayin ƙasar ɗaya ne, Ina tambayar kaina shin meye ya canza?

Babbar matsalar ƙasar nan ita ce masu faɗa a ji. Masu faɗa a jin Najeriya su ne suke fara furta kalaman da suke janyo rabuwar kai tsakanin mutane dake sassan ƙasar nan, kamar yadda muka gan su suna ta muhawara akan VAT, canza fasalin ƙasa, bawa yanki dama, maganar faɗan fulani kuma duk waɗannan abubuwa ne da za’a iya maganinsu cikin sauƙi. VAT zai samar da adalci tsakaninmu. Idan za mu canza fasalin ƙasar nan sai mun zama yan’uwa mu zama abu ɗaya babu bambancin komai kuma babu wanda yake neman dan’uwansa da sharri. Bayar da dama ga yanki domin kowa a dama da shi.

Abu ne mai sauƙi mu zauna mu tattauna hanyoyin da za mu samar da cigaba. Idan ka yi nasara ni ma na yi kuma gaba ɗayanmu za mu zama masu nasara. Za mu kawar da gaba, kowanne yanki zai ɗauki kowanne ɗan’uwa. Zan rufe da wata magana ta tsohon shugaban gwamnatin Birtaniya inda ya ce, “ya fi daɗi mu yi raha mu zauna ƙalau maimakon yaƙi.” idan wasu suka mamaye komai , muka ƙi manta yaranmu, kabilarmu, abincinmu, sai soyayya ta zama gaba maimakon raha sai faɗa.

Ba ma fin tsarin yadda ake gudanar da dimukraɗiyya a Amurka, ya ɗauki manyan ƙasar lokaci kafin su gyara dukkan matsalolinsu, kafin su zo da tsarin da ake amfani da shi yanzu a duniya akan yadda za’a gudanar da mulki cikin haɗin kai wanda yau shi ne duniya take amfani da shi.

Daga Karshe

Daga ƙarshe, bari na rufe wannan taro da ba ku wani takaitaccen labari. Wani uba ne da ɗansa yaron idan yana tare da yayansa idan zai yi fitsari zai dinga kiran sa Baba..Baba zan yi fitsari!”uban sai yake ganin kamar yana kunyata shi ne sai ya ba shi wata dabara wacce shi kaɗai ne da ɗan za su gane. Duk lokacin da kake jin fitsari ka zo ka ce min za ka ji waƙa, sai ka tafi ka yi fitsarin.

Sai yaron yake amfani da wannan tsarin . wata rana da ya yi tafiya sai ya umarci ƙannensa da su kula masa da yaron. Tsakar dare sai yaron ya tashi ya samu kawunsa ya ce masa “ina son jin waƙa” Sai kawun ya ce masa “yanzu dare ya yi da yawa baza’a kunna waƙa ba.” Yaron ya koma ya kwanta amma ya kasa bacci. Biladarsa ta cika , sai ya dawo yana roƙon kawun nasa yabar shi ya ji waƙa sai ya ce ka san dare ya yi zamu takurawa mutane amma kawo kunnenka na maka waƙar.

Na kawo wannan labarin ne domin babbar matsalar ƙasar nan ita ce ƙarancin bayani. Ba ma fito da abun da muke nufi kuma mafi akasari abun da muke faɗa ba shi muke aikatawa ba. Idan wasu suka ce suna son a samar da haɗin kai a ƙasar nan, sai ka ga ba haka suke nufi ba ko kaɗan, yanzu dai komai ya taɓarɓare a ƙasar nan za mu ci gaba da tafiya ne a haka? Shin muna son mu dinga ci gaba da rerawa muna son haɗin kai a yayin da muke taken Najeriya amma ba haka muke nufi ba?

Akwai buƙatar mu rufe ƙofa mu faɗawa kanmu gaskiya, mu fahimci gaskiya, ba wai kawai mu dinga haɗa zaman shan shayi ba, dole mu samar da tsare-tsaren da za su ba mu haɗin kai, dole mu ɗauki kowanne yanki dake ƙasar nan a matsayin abu ɗaya, mu yi aiki tuƙuru domin samar da daidaito a Najeriya mu bawa kowa dama iri ɗaya a Najeriya ba tare da duba inda mutum ya fito ba ko yarensa da yake magana da shi ba. Dole aiyukan raya ƙasar da gwamnati take samarwa su mamaye ko ina kuma a samar da adalci, dole mu ɗauki matakan haɗe kai. A cikin matakan ne aka samar da tsarin bautar ƙasa. Wannan na cikin abubuwan da suke haɗa kai muna fatan jihohi za su dinga karɓar adadin da aka tsara musu kowacce shekara tare da sama musu guraban aiki a jihohinsu domin kawo karshen kabilanci.

Har ila yau tsarin da muke ciki na ƙyashi da ƙoƙarin da kowanne yanki yake na hana ɗan’uwansa amfani da dukiyar da yake da ita na ɗaya daga cikin abubuwan da suke ba mu cikas a ƙasar nan. Dole mu tashi tsaye mu kauda wannan batun domin dukiyar ƙasa ta dukkan ƴan ƙasa ce. Idan babu batun wani yare ma ko al’uma, ba ma buƙatar Ibibios, Fulani, Igbo, Ijaw ko Hausa. Abun da muke buƙata shi ne Najeriya!

Akwai manyan abubuwan da wannan ƙungiyar ya kamata ta haɓaka domin ƙara samar da haɗin kai tsakanin mutanen ƙasar nan.

Ya kamata ƴan Najeriya su sani ba sai mun haɗu ido da ido ba, a ƙoƙarinmu na haɗa kai ba. Domin maƙiyanmu sun zare takubbansu dole mu haɗa hannu da aiki har mu kai ga murƙushe maƙiyanmu. Idan muka haɗa kai babu wanda zai yi nasara akan mu wannan ita ce Najeriya da muke buƙata, idan har manyan Amurka za su iya haɗe kansu duk da bambancinsu, mu ma za mu iya, za mu iya har mu samar da irin Najeriyar da kowa zai ti alfahari da ita.

Mun yi yaƙin basasa tare saboda ba ma bukatarsa, ya isa haka, yanzu ma lokacin da ya kamata mu haɗe kai mu yi amfani da bambancin dake tsakaninmu a matsayin makami da zamu kawo karshen kabilanci, akwai buƙatar mu fara daga yau mu sallama kanmu don tabbatuwar sabuwar Najeriya. Bari na rufe wannan bayani da ɗaya daga cikin kalmomin dake cikin tsohon taken Najeriya.

Najeriya muke ƙauna

Ƙasarmu ta gado

Muna da bambancin yare amma mu ƴan uwan juna ne.

Ina fatan za mu bar wajen nan da yunƙurin tabbatar da haɗin kai mu kuma yaɗa wannan saƙon, mu fara shirin samar da haɗin kai a ƙasarmu, mu kare haƙƙin kowa ko da wanne yare yake, wacce kabila ne da ma wanne addini yake bi. Gabaɗayanmu ƴan Najeriyane dole mu hada kai mu gina kasar mu, mai zaman lafiya da cigaba, Allah Ya taimake mu.

Na gode muku da sauraro. Ubangiji Ya mana albarka Ya albarkaci ƙasarmu Najeriya!

Comments
Loading...