For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Hanyoyi 10 Na Samun Nasara A Jarabawar JAMB Ta 2022

TASKAR YANCI hadin gwiwa da MURYAR BIRNIN KUDU sun yi nazari na musamman tare da tanada muku wadannan shawarwari domin samun nasararku, nasarar kannenku, nasarar ‘ya’yanku da ‘yan uwanku a jarabawar JAMB ta bana.

Akwai bukatar a tuna cewar an tsara jarabawar JAMB ne a kan maki 400 ga wanda ya cinye duk, saboda haka duk wanda ya sami maki 200 a JAMB kamar wanda ya sami maki 50 ne cikin 100 a wata jarabawar.

Yana iya yiwuwa kuma ma da yawa sun samu nasarar samun maki sama da 300 a JAMB, wannan kuma na samun asali ne daga irin shirin da dalibi ko daliba sukai kafin lokacin rubuta jarabawar, da kuma irin gudunmawar da makamantansu suka ba su lokacin da suke ba su darasi.

Sannan yana da kyau, mu tuna cewar, ana yin wannan jarabawar ne a kan komfiyuta, wanda hakan na nuni da cewar akwai bukatar dalibi da daliba su san yanda za su motsa komfiyuta ta yanda za su shigar da lambarsu da kuma zabar amsoshi.

Saboda haka akwai bukatar yin shiri na musamman da kuma tabbatar da an bi shirin domin samun nasara a jarabawar.

Ga shawarwarin da TASKAR YANCI hadin guiwa da MURYAR BIRNIN KUDU suka tanadar muku domin samun nasararku:

1. Fara Shiri (Plan) da Wuri: A yanzun nan ana kammala karanta shawarwarin a fara shiri (plan) da biyayya ga shirin.

2. Neman Samun Maki Mafi Yawa: A yi hasashen samun maki mafi yawa a jarabawar, kamar 300 zuwa sama. A dena tunanin bukatun makin jami’o’i.

3. Dakatar da Wasu Aiyuka Da Tunkarar Plan Gadan-Gadan: Akwai bukatar duk wanda zai rubuta jarabawar JAMB ya dakatar ko a dakatar masa da sauran aiyukan da za su ci masa lokacin karatu da nazari. A tuna cikin watanni 3 za a kammala a dawo a cigaba da sauran abubuwan bayan an samu gagarumar nasara.

4. Yin Karatu da Bita Bisa Tsari: A tsara yin karatu a kan darussan da aka zaba yayin yin rijistar JAMB din. A bibiyi Syllabus na JAMB domin sanin darussan da za a baiwa muhimmanci tare da yin amfani da littattafan da suka dace.

5. Tsarawa da Kula da Lokaci: A tsara lokutan bita na yau da kullum. A tsara lokacin kebancewa ai nazari na akalla awanni 4 a kullum, sannan a ware sauran lokuta kuma a bi su ba tare da sabawa ba tsawon lokacin da za a debe.

6. A Nemi Temako: Dalibi da daliba su nemi temako daga wajen malaman da suke da ilimin darussan da suka zaba, abokan karatunsu da suka iya abin da za su rubuta jarabawar a kai, na’urar komfiyuta da software ta training ga wadanda suka sami damar mallaka.

7. Bibiyar Tambayoyin da Suka Gabata: Akwai tambayoyin da suka gabata na wajen shekaru 40 wadanda mafi yawan sabbin tambayoyi na samo asali ne daga garesu. Ana iya samun wadannan tambayoyi a littattafai na musamman da aka shirya domin hakan, ana kuma iya samunsu a software ta training. Idan dalibi ko daliba suka sami nasarar yin kyakkyawan nazarin tambayoyi da amsoshin shekaru 10 na darussan da za su rubuta jarabawar a kai, akwai yiwuwar su sami maki sama da 300. Kuma nazarin mai yiwuwa ne duba da lokacin da ake da shi, idan har an fara shirin da wuri.

8. Neman Hadin Kan Iyaye da Malamai: Akwai bukatar iyaye su bayar da hadin kai wajen kyale ‘ya’yansu su bibiyi tsarin samun nasarar da suka tsarawa kan su. Akwai ma bukatar su kara musu karfin guiwa ta hanyar samar musu abubuwan da suke bukata domin samun nasara. Haka su ma malamai, za su iya temakawa ta hanyar dora dalibai kan hanyar samun nasarar da suke bukata.

9. Kauracewa Abokai, Guraren Hira, Kallace-Kallace da Wasanni: Duk da mun fadi makamancin wannan a baya, mun maimaita shi ne saboda matukar muhimmancinsa wajen samun nasarar bibiyar tsarin da aka tsara haka kuma ya kan kasance mai wuya. Haka kuma nazari zai tabbatar da cewa wadan nan abubuwa sune manyan abokan samun nasarar tsarikanmu. Saboda haka, idan muna son samun nasara mu san yanda za mu kyalesu ko da na wani lokaci ne.

10. A Matsa da Addu’a: Bayan an dage an tsara to kuma a matsa da rokon Allah ta hanyar da ta dace. Iyawar mutum kadai ba ta kai shi ga nasara sai Allah Ya yarda, to a nemi yardarSa, a nafilfili, a masallaci, a islamiyyu, a wajen almajirai, sannan a roki iyaye su dage da tayawa suma da addu’ar.

Kofar TASKAR YANCI da MURYAR BIRNIN KUDU a bude take domin bayar da shawarwari kan zabin jami’o’i, subjects da kwasa-kwasai.

Za ku iya tura mana sakon bukatarku a shafukanmu na Facebook: Taskar Yanci ko Muryar Birnin

Allah Ya bayar da nasara!

Comments
Loading...