For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Har Yanzu Ni Dan PDP Ne – Kwankwaso

Ana tsakiyar cigaba da tantama kan matsayinsa a jam’iyyar PDP, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya baiyana cewa, duk ya tabbatar da tattaunawarsa da jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP, har yanzu shi dan PDP ne.

Kwankwaso ya baiyana hakan ne a hirarsa da BBC, inda ya kara da cewa, tafiyar siyasar da ya kaddamar kwanan baya kadan, ‘The National Movement’ ita ce ta haifar da NNPP.

“A yanzu da muke magana, har yanzu ni dan PDP ne. Mun fara tafiyarmu ne mataki mataki. Da farko shine mu fara bari daga kasa, tunanin cewa wadansu a cikin jam’iyyar suna son ji kukanmu, amma jam’iyya ba ta yi komaiba; muka shiga tafiyar, kuma har yanzu babu abin da jam’iyyar ta yi, to yanzu muna matakin jam’iyya.

“Yanzu haka da nake magana da ku, muna tsakanin matafiya ne da kuma jam’iyyar siyasa, kuma ban bar PDP ba, amma wannan tafiyar tamu ta hade da NNPP.

“Maganar ba a kan Rabi’u Kwankwaso ko Kwansiyya ba ne. Magana ce ta ‘The National Movement’ kuma muna da yawa a cikinta, kuma mafi yawan mutanen da ke cikinta mutane ne masu tasiri, saboda haka ba zan yanke hukunci na ni kadai ba,” in ji Kwankwaso.

Lokacin da aka tambaye shi game da rushe shugabancin NNPP tun kafin su shiga jam’iyyar, Kwankwaso ya ce, “A gaskiya jam’iyyar ba tamu ba ce, amma suna sonmu mu zama a ciki. Shi yasa suke so su kawo wakilansu muma mu yi hakan. Kuma wa’adinsu ya cika, sannan duk sun sauka, ciki har da wanda yai mata rijista shekaru 20 da suka wuce.

“Saboda haka, sabon lale ne, kuma suna shigar da dukkanninmu saboda a mafi yawan jihohi ba su da kowa.”

Da yake mayar da martani kan maganar Kwankwaso, tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Bukola Saraki, ya nuna farincikinsa, inda ya ce, tsohon gwamnan Kanon zai cigaba da kasancewa a PDP.

“Na yi murna kasantuwar abokina Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa har yanzu shi ɗan Jam’iyyar PDP ne. Lallai ya yi abin da ya dace.

“Na tattauna da wasu cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP daga Kano – waɗanda suka kawo min ziyara makon da ya gabata a gidana dake Abuja, ina da ƙarfin gwiwa cewa Sanata Kwankwaso da tawagarsa za su ci gaba da zama cikin jam’iyyar don mu gina tare da ceto Nijeriya,” in ji Saraki a shafinsa na Facebook.

(DAILY TRUST)

Comments
Loading...