Wani dan bindiga ya bude wuta a wata jami’a a birnin Perm na kasar Rasha da safiyar Litinin din nan, inda ya kashe mutane biyar da raunata shida, a cewar kwamitin bincike na Rasha.
Ma’aikatar lafiya ta yankin Perm ta ba da rahoton cewa mutane 14 ne suka jikkata, duk da dai ba za iya cewa adadin ya tsaya haka ba.
Wanda ya aikata laifin, wanda ba a san ko wanene ba, ya yi amfani da bindigar da ba ta kisa ba, a cewar sashin yada labarai na Jami’ar Jihar Perm.
Dalibai da ma’aikatan jami’ar sun kulle kansu a cikin dakuna, yayin da jami’ar ta bukaci wadanda za su iya ficewa daga harabar su yi hakan.
Daga baya an kama tare da tsare dan bindigar, in ji ma’aikatar harkokin cikin gidan Rasha. Kwamitin bincike ya fara binciken kisan bayan faruwar lamarin.
Kamfanin dillancin labarai na Rasha, Tass, reshen jihar ya ambato wata majiya da ba a bayyana sunanta ba a cikin jami’an tsaro na cewa, wasu daliban sun tsallake harin ta tagogin wani gini.
Ma’aikatar lafiya ta yankin ta ce, daga cikin wadanda suka jikkata, a jikinsu akwai raunuka daga harbin da kuma wadanda suka samu a kokarin tserewa.