Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa, mutane 15 ne suka gamu da ajalinsu, baya ga wasu 11 da suka jikkata, a wasu hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a jihar.
Kwamishinan wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar jiya Jumma’a, ya ce, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne, sun kaddamar da munanan hare-haren a kauyuka hudu na jihar Kaduna.
Jaridar The Nation, ta ruwaito cewa, hare-haren sun faru ne ranar Alhamis, lokacin da ‘yan bindigar suka yiwa kauyukan kofar rago, domin karbar kudi, amma sai suka gamu da turjiya daga mutanen kauyen.