Sama da mutane 600 ne suka mutu sanadiyyar hatsarurruka a kan titin Kano zuwa Kaduna a tsakanin watanin Janairu da Yunin wannan shekara.
Assistant Corps Marshal da ke kula da Yanki na Ɗaya na Hukumar Kiyaye Hatsarurruka ta Ƙasa, Dr. Godwin Omiko ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyara wajen Maimartaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, a fadarsa da ke Zaria.
Dr. Godwin ya ce, ƙarin mutane 2,310 ne da hatsarurrukan suka rutsa da su suka sami raunuka daban-daban a cikin watannin.
Ya bayyana cewa, a watan Yuni na shekarar 2021, lokacin fitar da irin waɗannan bayanan, mutane 350 ne suka mutu a kan titin, amma a bana kuma al’amarin ya nunka, dalilin da ya jawo buƙatar kawo ziyarar.
Kwamandan Yankin, wanda ke kula da jihohin Kaduna, Kano, Katsina da Jigawa, ya buƙaci sarakunan da ke jihohin da su temaka wajen magance ƙalubalen.
“Maimartaba, samun gudunmawarku (wajen magance hatsarurruka) wani abu ne da ake tsananin buƙata, ganin yanda hatsarurrukan ke ƙaruwa a wannan yanki, duk da cewa, mun yi tarurrukan faɗakarwa da dama a tashoshi da sauran gurare amma kuma hakan bai yi tasirin da ake buƙata ba,” in ji shi.
Dr. Godwin ya bayyana cewa, hatsarurrukan na da alaƙa da tsula uban gudu, ganganci a overtaking, tuƙin ganganci, tuƙi bayan an bugu da kuma yin watsi da dokokin hanya da direbobi ke yi.
A jawabinsa, Sarkin Zazzau ya koka game da ƙaruwar mace-macen, inda yai kira ga hukumar da kar tai ƙasa a guiwa wajen faɗakarwa da kuma neman haɗin gwiwa domin ganin an shawo kan matsalar.
Sarki Bamalli ya kuma tabbatarwa hukumar cewa, masarautar zatai amfani da dukkanin hanyoyinta na faɗakarwa wajen ganin ta yi kira ga masu tuƙi domin magance matsalar.