Mutane biyu da suka hada da Bara’atu Garba da Mahmud Surajo sun rasa ransu a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da kwale-kwale mai dauke da fasinjoji 13 ya juye a Karamar Hukumar Ringim da ke Jihar Jigawa.
A lokacin hatsarin dai, fasinjoji biyar wadanda suna cikin wadanda aka ceta, an kwantar da su a asibiti, yayin da wasu shida daga cikin fasinjojin kuma har yanzu ba a gansu ba.
Hatsarin dai ya rutsa fasinjojin ne lokacin da suke kan hanyarsu ta kai ziyarar ta’aziyya.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar Yansandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiitu ya tabbatar da lamarin ga manema labarai a jiya Litinin.
Ya ce, “A ranar 11 ga Satumba, 2022, da misalin karfe 12:40 na rana, labarin da muka samu ya nuna cewa, wani kwale-kwale dauke da mutane 13 wadanda suke kan hanyarsu daga Dabi zuwa Siyangu duk a Karamar Hukumar Ringim ya kife.”
Ya kara da cewa, ‘yansanda na samu labarin hatsarin suka bazama wajen domin fara aikin ceton rai.
“Jami’an na isa wajen suka fara aikin bayar da temako tare da temakon direbobin yankin. Aikin ya sa an gano mutane bakwai inda aka garzaya da su Babban Asibitin Ringim domin a ba su kulawa. Mutum biyu daga cikin wadanda aka gano likitoci sun tabbatar da rasuwarsu,” in ji Shitu.
DSP Lawan Shitu ya bayyana Bara’atu Garba ‘yar shekara 30, da Mahmud Surajo dan shekara 3 a matsayin wadanda suka rasun, inda ya kara da cewa an mika gawarwakinsu ga iyalansu domin su yi musu sutura.
Ya kuma ce, sauran fasinjoji shidan kwale-kwalen ba a gano su ba a lokacin binciken, amma har yanzu ana ci gaba da bincike.
Haka kuma Shitu ya ce, binciken da aka gudanar ya nuna cewa, kwale-kwalen ya bugi wani abu ne a cikin ruwan, abun da ya sa ya wargaje.