Hukumar kiyaye afkuwar hatsura ta ce mutane shida ne suka mutu yayin da biyu suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya afku a ƙauyen Dinki da ke jihar Bauchi.
BBC Hausa ta rawaito cewa, hukumar ta ce hatsarin motar ya faru ne bayan wata mota ƙirar Peugeot ta ƙwace wa direbanta da misalin karfe 10 na safiyar Laraba.
Shugaban hukumar ta kula da hatsura a Bauchi, Yusuf Abdullahi ne ya tabatar da faruwar lamarin yana mai cewar sai da ya dauki jimai’ansu sa’a guda kafin su isa inda hatsarin ya afku don miƙasu a basu agajin gaggawa a baban asibiti na Bogoro.
Yusuf Abdullahi, ya kuma shawarci direbobi da su ringa kiyaye dokokin hanya da dokokin tuƙi a duk lokacin da suka hau abin hawa.