For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Hauhawar Farashi A Najeriya Ta Kai Kaso 21.09% A Lokacin Da Farashin Abincin Yai Sama

Hauhawar Farashi a Najeriya ta yi sama kaso 20.77% a watan Satumba, 2022 zuwa kaso 21.09% a watan Oktoba 2022 ana kuma tsaka da samun hauhawar farashin kayan abinci, in ji Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS.

Hukumar ta kuma ce, hauhawar farashin kayan abinci a watan Satumban da ya gabata yana matakin 23.34%, yayinda a watan Oktoba, 2022 ya kai kaso 23.72.

Hukumar NBS ta bayyana hakan ne a bayanan farashin siyar da kayayyaki, CPI, na watan Oktoba, 2022, da ta saki a yau Talata.

“A bayanan wata-wata, hauhawar farashi a watan Oktoba, 2022 ya karu da kaso 1.24%, wannan ya zo da 0.11% kasa da abun da aka gani a watan Oktoba 2022 wanda ya kasance kaso 1.36. Wannan ya nuna cewa a a gaba dayan watan Oktoba na 2022 farashin gaba dayan kayayyaki ya sauka da kaso 0.11,” in ji rahoton.

“Canjin da aka samu a CPI cikin watanni shabiyu da suka kare a Oktoba, 2022 shine kaso 17.86%, abun da ke nuna karuwar kaso 0.91% idan aka hada da kaso 16.96 idan aka kwatanta da watan Oktoba na 2021.”

Hukumar ta NBS ta alakanta matsayin hauhawar farashin a kan kudaden shigo da kayayyaki, tsadar kudin makamashi, hauhawar farashin kayan abinci da sauran su.

“A tsarin bibiya na shekara-shekara, a watan Oktoba na 2022, hauhawar farashi a birane ya kai kaso 21.63%, karuwar kaso 5.11% idan aka hada da kaso 16.52% a watan Oktoba, 2021. A tsarin wata-wata kuma, hauhawar farashi a birane yana kaso 1.33% a watan Oktoba na 2022, abun da ya zama raguwa da kaso 0.12% idan aka kwatanta da kaso 0.12% a watan Satumba na 2022.”

Comments
Loading...