For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Helkwatar Tsaro Ta Ce An Kashe ‘Yan Ta’adda 950 Da ‘Yan Bindiga 537 Cikin Watanni Bakwai

Helkwatar Tsaro a ranar Alhamis din nan, ta bayyana cewa an kashe ‘yan ta’adda 950 wadanda suka hada da manyan kwamandojinsu a tsakanin 20 ga watan Mayu na 2021 da 6 ga watan Janairun nan.

Ta kuma bayyana cewa, a dai wannan lokaci, an kashe ‘yan bindiga 537 da sauran masu laifuffuka wadanda suka hada da jagororin ‘yan bindiga guda biyu a jihar Zamfara, masu suna Alhaji Auta da Kachalla Ruga.

Mai Rikon Mukamin Darakta bangaren amfani da Kafafen Yada Labarai na Helkwatar, Major-General Benard Onyeuko ne ya bayyana hakan ga ‘yan jaridu a Abuja.

KU KARANTA: Abu Biyar Da Ba Ku Sani Ba Game Da Ƙasurgumin Ɗan Fashin Zamfara, Bello Turji

Ya kuma ce, sojojin sun kuma kubutar da wadanda akai garkuwa da su kimanin 1,000 tare da kwato makamai daga masu laifin.

“A cikin lokacin da ake magana, sojojinmu sun yi sanadiyyar mutuwar ‘yan ta’adda 950 wadanda suka hada da manyan kwamandojinsu da shugabanninsu. Haka kuma an kama ‘yan ta’adda 79, sannan kuma rundunar Hadin Kai ta ceto wadanda akai garkuwa da su guda 133.

“A bangaren Hadarin Daji kuma, sojojin samanmu sun samu nasara tsakanin 20 ga Mayu na 2021 da 6 ga Janairun 2022. ‘Yan bindiga 537 da sauran masu laifuka sojojinmu suka kashe.”

Comments
Loading...