For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Hisbah A Kano Ta Ce An Samu Karuwar Bokaye A Jihar

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta baiyana cewa, an samu karuwar bokaye a jihar ta Kano.

Hukumar ta baiyana haka ne a shafinta inda ta ce, ta kama akalla bokaye talatin a shekarar da ta gabata ta 2021.

Hukumar ta ce an gano karuwar yawan bokayen a jihar ta hanyar la’akari da yadda ƙididdigar bokayen take a baya.

Hukumar ta kara da cewa ta ja hankalin wasu daga cikin bokayen ta hanyar yi musu nasiha kuma daga bisani ta sake su, yayin da wasu daga cikin bokayen aka kai su kotu domin yi musu hukunci.

Haka kuma Babban Kwamandan Hukumar, Ustaz Haroon Ibn Sina, ya ja hankalin jama’a musamman mata da su kiyaye biyewa bokaye domin gudun sabawa Allah Madaukaki.

Comments
Loading...