For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Hisbah Na Neman ‘Yan Homo Masu Daura Aure A Kano, Ta Kama ‘Yan Biki 19

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama matasa 19 a wajen biki a tsakiyar birni bisa zargin halartar bikin auren jinsi.

TASKAR YANCI ta gano cewa, wadanda ake zargin, wadanda ke zama ‘yan shekaru 20 zuwa sama kadan, sun halarci wajen bikin ne domin shaida auren wasu maza biyu da ake zargin ‘yan homo ne masu suna Abba da Mujahid.

An rawaito cewa, jami’an Hisbah sun kai mamaye wajen bikin ne kafin a fara gundarin daurin auren, inda suka kama ‘yan mata 15 da kuma samari 4.

Da yake tabbatar da lamarin, Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Harun Ibn Sina ya ce, an kai mamayen ne bayan sun samu bayanai daga wani mazaunin wajen.

Ibn Sinan ya ce, wadanda ake zargi da auren juna, Abba da Mujahid, sun tsere bayan bayyanar jami’an hukumar.

Ya kara da cewa, wadda ta hada bikin, Salma Usman ‘yar shekara 21 tana hannu, yayin da hukumar ke ci gaba da dagewa wajen ganin an kamo Abba da Mujahid.

Ya kuma ce, Hukumar Hisbahr zata mika wadanda ke tsaren ga rundunar ‘yansanda domin yin abin da ya dace, saboda mafi yawan ‘yan matan sun bayyana cewa su an gayyace su daurin auren ne daga jihohi makwabta.

Comments
Loading...