For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Hukumar Alhazai Ta Sanar Da Kudin Hajji Da Ranar Rufe Rijistar Alhazai A Bana

Hukumar Kula da Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta sanar da kudin zuwa hajjin bana ga maniyyata zuwa aikin hajjin shekarar 2023.

Da yake sanar da manema labarai a yau Juma’a a Abuja, Shugaban NAHCON, Zikrullah Hassan, ya ce, kudin hajjin bana bai zama bai daya ba kamar yanda yake a shekarun baya, ya kara da cewa, kudin hajjin bana an yanke shi gwargwadon jihohin Najeriya.

A cewarsa, duk wani maniyyaci dake jihar Borno da Adamawa, zai biya kudin hajjin bana naira miliyan 2,890,000.

Zikrullah Hassan, ya kara da cewa, maniyyata daga sauran jihohin Arewacin Najeriya, zasu biya kudin hajjin bana naira miliyan 2,919,000.

Maniyyatan da suke jihohin yankin Kudu-maso-Gabas, in banda Jihar Cross River, zasu biya kudin hajjin bana naira miliyan 2,968,000.

Wadanda suke daga Jihar Cross River kuma zasu biya naira miliyan 2,943,000 a matsayin kudin aikin hajjin bana in ji shugaban na NAHCON.

Yayinda su kuma maniyyatan da suke jihohin Ekiti da Ondo zasu biya naira miliyan 2,888,000, su kuma maniyyata daga jihohin Lagos, Ogun da Oyo zasu biya naira miliyan 2,993,000 a matsayin kudin aikin hajjin bana.

Shugaban na NAHCON ya kara da cewa, ranar karshe ta karbar kudin hajjin na bana tana nan a 24 ga watan Afirilu, 2023, inda ya kara da cewa ba za a kara wa’adin karbar kudaden ba.

Comments
Loading...