Hukumar Hana Fasakwauri da Kasa ta bayyana cewa za ta bude bayar da dama ga ‘yan kasa domin neman kasancewa cikin jerin ma’aikatan da za ta diba.
Hukumar ta sanar da hakan ne a tare da sunayen sabbin ma’aikatan da ta diba a matakai daban-daban wanda aka wallafa DailyTrust.
Hukumar ta sanar da cewa za ta bude damar diban sabbin ma’aikatan daga ranar Litinin 13 zuwa Juma’a 24 ga watan Disambar wannan shekara.
Masu sha’awar neman aikin za su ziyarci shafin daukar ma’aikata na hukumar http://www.vacancy.customs.gov.ng domin cikewa da zarar an bude.
Haka kuma sanarwar na dauke da bayanin cewa, wadanda sunayensu suka fito a sunayen da aka saki, za su je Ofishin Shugaban Hukumar da ke Old Federal Secretariat, Area 1, Garki, Abuja daga ranar Litinin 8 ga watan Nuwamba zuwa Litinin 7 ga watan Disamba na wannan shekarar domin ajjiye bayanansu (documentation).
A karshe hukumar ta gargadi mutane da cewa, hanyar neman aiki a hukumar a bude take ga kowa kuma ba a bukatar bayar da kudi kafin a dauki mutum aikin.