For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Hukumar Customs Ta Tsaurara Tsaro A Boda Don Hana Shigo Da Shinkafa

Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Najeria, ta matsa matakan tsaro a iyakokin Najeria ta hanyar tura jami’anta musamman zuwa iyakokin Najeriya da Jamhoriyar Benin da kuma sauran iyakoki.

Hukumar ta ce ana yin yunkurin ne domin magance matsalar masu fasakwaurin shinkafa.

Wannan cigaban ya zo ne, awanni 24 bayan Darakta Janar na Kungiyar masu Samar da Shinkafa ta Najeriya, ANDY Ekwelega, ya ce an shigar da shikafa kasar Benin mai yawan da ya haura ton 566,000 daga kasar Thailand da India.

Ekwelega ya bayyana cewa kusan dukkan shinkafar da ake shigar da ita kasar Benin ana yiwowa fasakwaurinta ne zuwa Najeriya saboda yawan jama’ar kasar da kuma girman kasuwa.

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar a ranar Lahadi cewa, akwai karuwar fasakwaurin shinkafa zuwa Najeriya.

Dalilin haka, gwamnatin ta ce, ta kira zaman tattaunawa da Hukumar Hana Fasakwaurin da sauran jami’an tsaro domin a tsara yanda za a magance mummunar matsalar.

Da yake magana da wakilin PUNCH, Mataimakin Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Najeriya, Timi Bomodi ya ce, “haka abin ya ke kasancewa a karshen shekara, mun yi tsammanin hakan kuma za mu kara tura jami’ai zuwa iyakokin domin mu magance fasakwaurin.”

Bomodi wanda yai magana da wakilin PUNCH a shelkwatar hukumar a Abuja, ya ce har yanzu ba a yanke adadin jami’an da za a tura ba, amma dai za a debo jami’an daga kowanne sashi na hukumar.

Ya kuma ce Hukumar tare da Gwamnatin Tarayya na yin aiki tare da hukumomin kasar Benin domin magance matsalar.

Ya kara da cewa, hukumar ta yi amfani da tsare-tsaren ECOWAS na safarar kayayyaki tsakanin kasashe, sannan tana aikin wayar da kai domin fahimtar da al’umma matsalar fasakwauri.

Comments
Loading...