Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta sako matar Gwamnan jihar Kano, Hafsat Abdullahi Ganduje bayan bincikenta da tai kan zargin cin hanci da rashawa da danta Abdulaziz Abdullahi Umar Ganduje ya shigar gaban hukumar.
Jaridar NAGERIANTRACKER ta rawaito cewa, yanzu haka matar Gandujen tana Gidan Gwamnatin Kano inda ta shirya domin cigaba da aiyukanta.
JAKADIYA ta rawaito a baya cewa, jami’an hukumar EFCC sun kama matar Gandujen a Litinin da yamma bayan ta ki amsa gayyatar da hukumar tai mata.
NIGERIAN TRACKER ta yi kokarin tuntubar mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwajuren, sai dai bai amsa kiranba, amma daga baya ya sanar da jaridar cewa zai tuntubesu daga baya.