For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Hukumar Immigration Reshen Kano Ta Samu Sabon Kwantirola

CIS Mu’azu Abdulrazak ya karbi ragamar kula da aiyukan Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (Nigeria Immigration Service) reshen jihar Kano a matsayin sabon kwantirola, yayinda akai kira domin samun goyon bayan al’umma wajen samun ingancin tsaro a cikin kasa da kuma bakin iyakoki.

A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar reshen jihar Kano, Nura Musa Ya’u ya sanyawa hannu, an baiyana cewa, sabon kwantirola CIS Mu’azu ya karbi aikin ne daga CIS Bello Garba wanda akaiwa canjin wajen aiki zuwa jihar Katsina.

Sanarwar ta rawaito sabon kwantirola Mu’azu wanda ya dawo jihar Kano daga Katsina yana kira ga masu ruwa da tsaki da kuma sauran al’umma da su ba shi goyon baya wajen ganin ya samu nasara.

Kwantirola Bello Garba wanda ya mika ragamar aiki ga kwantirola CIS Mu’azu, ya godewa jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya reshen jihar Kano da al’ummar jihar Kano bisa goyon bayan da suka ba shi lokacin yana kwantirola a jihar.

Comments
Loading...