Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC a ranar Litinin ta bayyana cewa tana da karfin iya kula da zaben fidda gwani ta hanyar ‘yartinke indan jam’iyyu za su gudanar da tsarin.
Kwamishinan hukumar mai kula da yada labarai, da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye, ya fadawa jaridar The Nation cewa, jam’iyyu ke da alhakin shiryawa da kuma gudanar da zaben fidda gwanayensu, ita kuma INEC aikinta shine kula da yanda ake gudanar da wannan zabe na fidda gwanaye.
Ya ce hukumar ta saba cimma bukatun kula da gudanar da zaben fidda gwanaye da jam’iyyu ke yi.
Okoye ya ce, “jam’iyyun siyasa ke da alhakin gudanar da zaben fidda gwanaye. Aikinsu ne su tanadi wajen gudanar da zaben. Kuma su suke da alhakin samar da tsaro ga harkokin zabensu.
“Su suke da alhakin buga takardun gudanar da zaben da kuma tanadar akwatin kada kuri’u da rumfunan kada kuri’un.
“Aikinsu ne su yanke cewa, ko za su yi amfani da mazabu 8,809 ko kananan hukumomi 774 a matsayin guraren gudanar da zaben fidda gwanayensu.
“Aikin da yake kan hukumar zabe bas hi da yawa. Aikinmu shine kula da yanda za a gudanar da zaben fidda gwanayen kamar yanda dokokin da jam’iyyun suka sa suke.
“Muna da karfin iya kulawa da zaben ta hanyar ‘yar tinke ko ba ta shi ba. Mun yi hakan a baya, kuma muna da kwarewa da karfin iya cigaba da aiwatar da abubuwan da doka ta tanada.