For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Hukumar INEC Ta Sauyawa Ma’aikata 186 Guraren Aiki

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce ta gano shugabannin sassa 46 da maikata 140 domin gaggauta yi musu sauyin gurin aiki.

Shugaban Sashin Yada Labarai da Wayar da Kan Masu Zabe, Festus Okoye, ne ya baiyana hakan a wata sanarwa jiya Juma’a.

Ya ce, an yi canje-canjen guraren aikin ne a fadin Najeriya saboda a tabbatar da gamsasshe kuma ingantaccen aiki.

“Ma’aikatan da abin ya shafa sun kasance ko dai suna aiki a jihohinsu ko kuma sun debe tsakanin shekaru 10 zuwa 32 suna aiki a jihar da suke.

“Hukumar ta gano cewa wannan yanayi bai dace da yanayin aikin da ake bukata su yi ba,” in ji Okoye.

Ya kuma ce, duba da tsare-tsaren tura ma’aikata wajen aiki na hukumar, babu wani shugaban sashi da zai aiki a jiharsa ta haihuwa.

Okoye ya kara da cewa, “Haka kuma, babu wani ma’aikaci da zai aiki sama da zagayen zabe biyu a mukami ko waje daya ba. A kan haka, hukumar ta gano ma’aikata 186 da suke buƙatar gaggauta sauya musu guraren aiki.”

Ya ce, ma’aikatan da aka yiwa sauyin wajen aiki zasu kammala barin wajen aikin da kuma fara aiki a sabbin guraren aikin nan da 9 ga watan Maris, 2022.

Ya kara da cewa, aikin tantance masu bukatar sauyin wajen aikin yana cigaba da gudana kuma zai tabo sauran sassa na hukumar.

(DAILY TRUST)

Comments
Loading...