Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta ki karbar Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello a matsayin sabon Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar All Progressive Congress, APC.
INEC ta baiyana matsayarta ne a kan wata wasika mai taken, Re: Invitation to the emergency meeting of the National Executive Committee’, wadda Sakataren Hukumar, Rose Omoa Oriaran-Anthony.
Wasikar da ke dauke da kwanan watan 9 ga watan Maris, 2022, a matsayin amsar wasikar gaiyatar da jam’iyyar ta yiwa INEC zuwa zaman shugabannin jam’iyyar, inda za a tabbatar da Abubakar Sani Bello a matsayin sabon Shugaban Kwamitin Riko na APC.
Wasikar APCn na dauke da sanya hannun Abubakar Sani Bello da Tahir Mamman wanda aka rawaito cewa an nada shi a matsayin sabon Sakataren Kwamitin Riko na Jam’iyyar.
Haka kuma, INEC a wasikar ta baiyana cewa ba ta san an samu canjin shugabanci ba a APC, saboda haka ba za ta mutumta gaiyatar tunda ba wadanda ta sani ne, Shugaban Kwamitin Riko, Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, da Sakatare, John Akpanudoedehe ne suka sanyawa takardar hannu ba.
“Hukumar INEC na jawo hankalinku cewa, sanarwar da kuka gabatar ta zaman tattaunawa ba ta samu sanya hannun Shugaban Jam’iyya na Kasa, (Buni) da kuma Sakatare na Kasa, (Akpanudoedehe) na Kwamitin Riko na Jam’iyyar (APC), sabanin tanadin doka na 1.1.3 na Dokokin Hukumar (INEC) na 2018 da suka shafi alaka da jam’iyyu.
“Haka kuma, ana tunawa jam’iyyar APC tanadin doka da sashi na 82 (1) na Dokar Zabe ta 2022, wanda ya bukaci sanarwa a kalla kwana 21 kafin taron kasa, taron jiha, zaman tattaunawa da aka shirya domin yin hadaka, da zaben shugabanni ko wasu jami’an gudanarwa ko nada wani dan takara mai neman shugabanci,” in ji wani ɓangare na wasikar INEC.
INEC ta bukaci APC da ta kula da abubuwan da aka baiyana tare da tabbatar da yi musu biyayya.