Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB ta canza ranar fara rijistar jarabawar UTME da DE na shekarar 2022 zuwa 19 ga Fabarairu.
Wannan ya zo ne, awanni 24 bayan hukumar ta tabbatar da cewar ba za ta canza lokacin ba daga 12 ga Fabarairu duk da dakatar da rijistar katin dan kasa da akai saboda matsaloli.
Hukumar a jawabin da ta gabatar a yau Talata ta ce, canza ranar fara jarabawar daga 12 ga Fabarairu ya samo asali saboda a kara inganta al’amura.
Jawabin da mai magana da yawun hukumar, Fabian Benjamin ya ce, “Shirin rubuta jarabawar, wanda za a kammala a karin sati daya, an yi hakanne domin a saurari shawarwarin dalibai da masu ruwa da tsaki.”
“Duba da wannan canji, sabon jadawalin yanda za a gudanar da rijista da jarabawar za a baiyana shi a ranar Litinin mai zuwa 14-02-2022.
“Ana sanar da masu sha’awar cike JAMB da DE da su nuna lura wajen biyayya ga tsarin yin rijistar kamar yanda hukumar za ta fitar”.
Hukumar ta tabbatar da cewa babu wanda zai sami damar yin rijistar JAMB ko DE ba tare da ya mallaki shaidar kasancewa dan kasa ta NIN ba.