For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Hukumar Kula Da Jiragen Ƙasa Ta Najeriya Ta Dakatar Da Zirga-zirga A Titin Abuja-Kaduna

Hukumar Kula Da Titunan Jiragen Ƙasa ta Najeriya, NRC, ta dakatar da zirga-zirgar jiragen ƙasa na wani lokaci a kan titin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna.

Hukumar NRC dai ta yanke wannan hukunci ne saboda faruwar abin da ba ai tsammani ba.

Sanarwar hukumar ta fito ne yau Talata da safe.

An rawaito cewa ƴan ta’adda sun kai hari kan titin jirgin ƙasan inda suka tayar da bom abin da ya shafi wani jirgi mai dauke da mutane kusan 900 a kauyen Rijana da ke Kaduna.

Ƴan ta’addar sun kai harin ne a jiya Litinin da daddare.

NRC, a sanarwar da ta saki a shafinta na Twitter a yau Talata ta ce, “Zuwa ga fasinjoji, saboda wani alamari da ba a zata ba, zirga-zirgar jirgin ƙasa a kan titin Abuja-Kaduna ta dakata na wani lokaci.

“Za a gabatar da bayanai game da lamarin a lokacin da ya dace.”

Comments
Loading...