Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa, NDLEA ta ce, ta samu nasarar kama kwayoyi miliyan daya da rabi na abin maye da suka hada da Tramadol, Exol-5 da Diazepam an doro su a mota daga garin Onitsha na jihar Anambra da nufin kaiwa Yauri ta jihar Kebbi.
Daraktan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Helkwatar NDLEA, Abuja, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a yau Lahadi, inda ya ce an kama miyagun kwayoyin ne a jihar Edo, a ranar Juma’ar da ta gabata.
Daraktan ya kuma ce, a dai wannan rana, an kama kwayoyin Diazepam a Segemu da ke Kano.
KU KARANTA: ‘Yansanda A Zamfara Sun Kama Masu Ci Da Siyar Da Naman Mutane
Ya kuma ce a satin da yake karewa, an kama kudade kimanin naira 1,413,344 da kuma makamai da ake zargin na wani babban dan bindiga ne kuma dan kwaya a jihar Plateau.
An kama direban motar da dauko kwayoyin zuwa Kebbi mai suna Bashir Lawwali dan shekaru 30 tare da wani Abubakar Sani dan shekara 30 shima, da kuma Ali Abubakar mai shekaru 19.
Yayinda kwayoyin da aka kama a Kano, an kama su ne a hannun wani da ake kira da Sa’idu Yahaya mai shekaru 31.