Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya ta ce ta samu nasarar kama wadanda ake zargi da ta’ammali da miyagun kwayoyi har mutum 134 a jihar Jigawa.
Hukumar ta kuma sanar da cewa, ta samu nasarar kwato miyagun kwayoyin da nauyinsu ya kai kilogram 5.970 a jihar.
Kwamandar Hukumar a Jigawa, Maryam Sani ce ta bayyana hakan a wani taron manema labarai a Dutse a Litinin din nan.
Kwamandar ta ce, wadanda ake zargin an kama su a mabanbantan lokuta da kuma mabanbantan gurare a lokutan sumamen da jami’an hukumar sukai a jihar tsakanin 27 ga Satumba da 10 ga Oktoba a dukkanin kananan hukumomi 27 na jihar.
Ta bayyana cewa, sumamen ya biyo bayan umarnin da shugaban hukumar ta kasa, Buba Marwa ya bayar domin magance matsalar masu ta’ammali da miyagun kwayoyi a kasa gaba daya.
Kwamandar ta ce, cikin wadanda aka kama akwai, jami’an tsaro, ma’aikatan gwamnati, dalibai da kuma mata guda 2.
Maryam Sani ta ce, kashi 90% na wadanda aka kama masu amfani da miyagun kwayoyin ne, inda aka yi musu nasiha da gargadi aka kuma sake su.
Kwamandar ta tabbatar da kudirin hukumar NDLEA a Jigawa na kawo karshen matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin al’ummar jihar.
NAN