For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Hukumar Tace Fina-Finan Kano Ta Hana Dora Fina-Finan Kannywood Da Ba A Tace Ba A Youtube

Hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ta ce daga yanzu babu wani fim mai dogon zango da za ta bari a dora a Youtube ba tare da an kai mata ta tace shi ba.

Shugaban hukumar, Isma’il Na’abba Afakallah, ya shaida wa BBC Hausa cewa sun dauki matakin ne sakamakon yadda ake sakin wasu fina-finai da suka ci karo da al’adu da addinin mutunen jihar ta Kano.

“Muna magane ne a kan yadda sakin fina-finai ya zama ruwan-dare a manhajar YouTube wanda kuma yake zama illa ga tarbiyya, kuma dole ne mu dauki mataki a kan harkar nan ta fina-finai da wakoki da abubuwan da suka shafi dangogin rubuce-rubuce,” in ji shi.

Afakallah ya kara da cewa matakin da suka dauka ya hada da duk wani fim mai dogon zango da za a dauka a wasu wurare amma daga bisani a kai jihar ta Kano.

Shafawa Jigawa Kashin-Kaji

Ita ma Jihar Jigawa da ke makwabtaka da jihar Kano ta dauki irin wannan mataki, inda ta umarci masu shiryawa da daukar fim, ko rera wakoki na siyasa da na soyyaya ko na fim, da masu yi musu rawa da su dakatar da harkokinsu a jihar har sai sun yi rijista da hukumar.

Daraktan hukumar tace fina-finai ta jihar, Yusuf Magaji, ya shaida wa BBC cewa sun dauki matakin ne bayan daraktan fim din nan mai suna ‘Makaranta’ ya bayyana cewa a jihar ya dauki fim din.

Fim din ‘Makaranta’ ya nuna abubuwa da dama da ɗumbin jama’a suke ganin ba su dace a yi fim a kansu ba, wadanda suka hada da madigo da batsa da makamatansu.

“Mun yi haka ne saboda mu tantance wadanda suke shigowa jihar. Akwai wani fim da aka shirya wai shi ‘Makaranta’ inda shi wanda ya shirya shi jihar Kano take nemansa ruwa a jallo, sai yake cewa ba a Kano ya shirya ba, a Jigawa ne. A gaskiya bai zo wurinmu ya nemi izinin shirya fim din ba,” a cewar Yusuf Magaji.

Ya kara da cewa daraktan ya yi furucin ne da zummar shafawa Jigawa kashin-kaji don haka su ma daga yanzu ba za su bari a rika yin abubuwan da suka keta dokoki da al’adun jiharsu ba.

Amincewa Da Sabuwar Doka

Masu shirya fina-finai masu dogon zango sun bayyana amincewarsu da wadannan matakai da gwamnatocin jihohin Kano da Jigawa suka dauka, suna masu yaba wa matakan.

Lawan Ahmad, tauraron fim ne kuma mai shirya fim din dogon zango na Izzar So, kuma ya shaida mana cewa su dama sai sun mika fina-finansu an tantance kafin su sanya a YouTube.

“Mu dama can muna bayar da fina-finanmu a duba. Sai dai idan an samu tsaiko ko wata matsala saboda yanayin aiki shi ne za ka ga ba mu bayar ba. Amma maganar gaskiya yadda wasu suke amfani da YouTube wajen saka abubuwan da ba su dace ba, ya kamata a sanya musu ido,” in ji shi.

A cewarsa matakin da hukumar tace fina-finai ta dauka yana da amfani “saboda kare al’ada da addininmu.”

Daga: BBC Hausa

Comments
Loading...