For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Ta Kano Ta Kama Mutane 8 Da Zargin Karkatar Da Naira Biliyan 4

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Al’umma da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta tabbatar da cewar, ta kama mutane takwas da ake zargi da karkatar da kuɗaɗen da yawansu ya kai naira biliyan huɗu na Kamfanin Samar da Kayan Noma na Kano.

Shugaban Hukumar, Muhuyi Magaji Rimingado ne ya tabbatar da haka a yau Asabar, inda ya ce, hukumar ta ƙaddamar da bincike domin gano yanda suka karkatar da kuɗaɗen.

Rimingado ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake ziyartar gidan ajjiya na kamfanin.

Labari Mai Alƙa: An Damƙe Mai Yin Takin Zamanin Bogi, Yana Sawa A Buhun Takin Zamanin Gaske

Ya yi zargin cewa, kuɗaɗen an tura su daga asusun Kamfanin Samar da Kayan Noma na Kano zuwa wata ƙungiya, wadda Hukumar Yiwa Kamfanoni Rijista, CAC ta yi mata da rijista da sunan Ƙungiyar Amintattun Abokai (Association of Compassionate Friends).

Ya ƙara da cewa, an kafa ƙungiyar ne da manufar samar da kyakkywar rayuwa ga ƙananan yara da marassa ƙarfi, amma ake amfani da ita wajen aikata almundahana da kuɗaɗen al’umma.

Ya tabbatar da cewar an kama mutane takwas da ake zargi da hannu a cikin badaƙalar, inda ya ce suna bayar da bayanan da ake buƙata yanda ya kamata.

Rimingado ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano, musamman ma’aikata da su miƙa bayanan da zasu temaka wajen ƙwato kuɗaɗen gwamnati da kadarorin da aka sace, inda ya tabbatar da cewar za a ba su kariyar da ta kamata.

Comments
Loading...