Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Jigawa ta sanya sabbin dokoki domin rage rigingimun manoma da makiyaya a jihar.
Rundunar karkashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Aliyu Saleh Tafida PSC, ta sanar da cewa domin rage rigingimun makiyaya da manoma a jihar ta haramta kiwon dare da kiwon yara kanana a jihar.
A sanarwar da mai Magana da yawun ‘yan sandan, Lawan Shiisu Adam ya fitar, ta bayyana cewa ba za a amince da masu kiwo dauke da kwari da baka ba.
Haka kuma kuma sanarwar ta hana al’adar ‘dabaldi’ wadda matasa maza kadai ke fita kiwo ba tare da mata da manya ba.
Sanarwar ta kuma yi kira ga manoma da kar su dau doka a hannunsu, tare da yin kokarin sanar da duk wata matsala da suka hango na iya faruwa ga hukumomi.
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa, za ta mayar da martani a duk lokacin da suka kama wani makiyayi da kwari da baka ko kuma yana harbin mutane ko ‘yan sanda.