Humkumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta sanya ranar 25 ga watan Fabarairu a matsayin ranar gudanar da zabubbukan cike gurbi a mazabu shida da ke jihohi hudu.
Kwamishinan Hukumar INEC na Kasa kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar da Kan Masu Zabe, Festus Okoye ne ya bayyana hakan jiya Juma’a a Abuja bayan kammala zaman shugabannin hukumar ta INEC.
Zabubbuka shidan da za a gudanar sune na mazabar majalissar tarayya ta Akure ta Arewa/Akure ta Kudu a jihar Ondo; mazabar majalissar tarayya ta Jos ta Arewa/Bassa a jihar Plateau; mazabar majalissar jiha ta Ngor-Okpala a jihar Imo da kuma mazabara majalissar tarayya ta Ogoja/Yala da mazabar majalissar jiha ta Akpabuyo duk a jihar Cross River.
KU KARANTA: APC Ta Sa Ranar 25 Ga Fabarairu Domin Zaben Shugabaninta Na Kasa
Za a gudanar da zabubbukan ne sati biyu bayan zaben shugabannin kananan hukumomi na Birnin Tarayya Abuja wanda aka saka ranar 12 ga watan Fabarairu domin gudanarwa.
Kwamishina Okoye ya kuma ce hukumar zabe za ta hade zaben mazabar majalissar jiha ta Ekiti ta Gabas ta Daya da zaben gwamnan jihar wanda aka sa yinsa ranar 18 ga watan Yuni mai zuwa.
Hukumar Zaben ta kuma gargadi jam’iyyu da su guji gabatar da ‘yan takarkarun da ba su cancanta ba domin zabubbukan.
Ya bayyana cewa, hukumar tana tuntubar jami’an tsaro da kuma masu ruwa da tsaki game da gurbin mazabar majalissar jiha ta Shinkafi a jihar Zamfara, inda ya kara da cewa, har yanzu kakakin majalissar jihar Kaduna bai ayyana gurbin mazabar majalissar jiha ta Giwa ba.