For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

ICPC Ta Gano Cushen Naira Biliyan 400 Da Albashin Bogi Naira Biliyan 50 A Kasafin Kudi

Hukumar ICPC da ke kula da aiyukan cin hanci da rashawa da sauran laifuffukan da suka danganci haka, a jiya Alhamis ta ce kasafin kudin shekarun 2021 da 2022 sun fuskanci cushe ta hanyar maimaita aiyuka a ma’aikatu da ressa da suka kai kimanin naira biliyan 400.

Haka kuma, Hukumar ta ce ta gano cewa, an ware naira biliyan 49.9 a matsayin albashin ma’aikatan bogi a rabin farko na kasafin kudin shekarar 2022.

Shugaban Hukumar ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da Kwamitin Kudi na Majalissar Dattawa a shirye-shiryen gabatar da kasafin kudin shekarar 2023 a zauren majalissar a Abuja.

Duk da dai bai fayyace ma’aikatun da abun ya shafa ba, Owasanoye ya bayyana cewa an yi cushen kudin maimaita aiyuka na kudi naira biliyan 300 a kasafin kudin 2021; sannan kuma an yi cushen naira biliyan 100 a kasafin kudin shekarar 2022.

Owasanoye ya ce, ta hanyar bincikar kasafin kudaden ma’aikatu, ICPC ta kubutar da gwamnati daga asarar biliyoyin nairori a aiyukan karya.

Ya kuma yi kira ga Majalissar Tarayya da ta sanya ido sosai domin magance cushen maimaita aiyuka a kasafin kudin shekarar 2023 na naira biliyan 19.76.

Comments
Loading...