For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

‘Ina Maka Fatan Kasancewa Lafiya’, Tinubu Ya Taya Atiku Murnar Cika Shekara 76 A Duniya

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu ya taya abokin hamayyarsa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar murnar cika shekara 76 a duniya a ranar Juma’a.

Tinubu ya mika sakon fatan alkhairinsa ga Atikun ne ta kafar Twitter, awanni kadan bayan ya yiwa tsohon Mataimakin Shugaban Kasar gatse kan yawan tsayawarsa takarar neman shugabancin Najeriya.

A yammacin jiya Juma’ar, Tinubun ya rubuta cewa, “Ina taya dan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar murnar cika shekara 76 a duniya. Inai masa fatan kasancewa lafiya.”

Kafin wannan lokaci dai, Bola Tinubu ya yi jawabi a taron tattaunawa da Masu Ruwa da Tsaki na Yankin Niger Delta wanda aka gudanar a Gbaramatu, na Jihar Delta State, inda yai bayani ga Pere na Masarautar Gbaramatu, Oboro-Gbaraun II (Aketekpe, Agadagba) a kan tsare-tsarensa ga al’ummar Gbaramatu.

Tsohon gwamnan Legos din ya ce, “Ka yi bayanin samar da babbar tashar jirgin ruwa, tituna, gada da jami’a, dandalin masana’antu a Ogidigben. Wadannan ne suka zo zuciyarka, Kabiyesi, da duk wadanda suke nan.”

“Kabiyesi, Mai Martaba, na tsaya a gabanka, ba mu da yawa wadanda muka rage cikin masu yin takara. Wani ya ce Atiku ne. Sau nawa yana tsayawa takara? Ko yaushe tsayawa yake yi kuma har ya gaji. Ku fada masa ya je ya zauna. Ya isa haka.”

Comments
Loading...