Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya goyi bayan kiraye-kirayen da ake yi na amfani da intanet wajen tura sakamakon zabe a kasar.
A cewarsa, tsarin zai tabbatar da ba iya ma ‘yancin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ba har ma zai sa zabe a kasar ya zama sahihi.
Ya jaddada cewa yana da wahala yarda da masu adawa da suka kan tura sakamakon ta intanet duk da cigaban da fasahar zamani ta kawo.
Jonathan yayi maganar ne yayin da yake gabatar da lakca a ranar Laraba a wurin bikin Kaddamar da Dalibai na Kwalejin Tsaro ta Kasa, Rukuni na 30, a Abuja.
Ya ce, “Babu shakka ‘yancin kai na hukumar gudanar da zabe shine babban jigon da dimokuradiyya mai ci gaba ta dogara da shi.
“A Najeriya, hukumar da kundin tsarin mulki ya dorawa alhakin hakan ita ce Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa.
“Akwai bukatar wadanda ke da hannu a cikin garambawul na dokar zaben da ke gudana su duba iyakokinsu su kuma su yiwa kan su tambayoyi na gaskiya.
“Ta wannan hanyar, za su iya tantance ko suna ci gaba da bin tafarkin dimokuradiyya ta hanyar yin aiki don habakawa da kare ayyukan da tsarin mulki ya ba da tabbacin su cewa na INEC ne ko kuma neman mamaye damar hukumar, wanda hakan zai iya yin illa ga aiwatar da ‘yancinta. wajen gudanar da zabe.
“A koyaushe ina yawan cewa, tura sakamakon zabe ta intanet ita ce hanyar da za mu bi, idan da gaske muna son tabbatar da sahihancin ingancin zabenmu.
“Don haka, yana da wahala a fahimci dalilin da ya sa ake ci gaba da jayayya game da yiwuwar watsa sakamakon zaben ta hanyar intanet, duk da ci gaban da aka samu a fasahar tura bayanai, tsawon shekaru.
“Idan da gaske muna son karfafa tushen dimokiradiyya a cikin kasarmu, bai kamata mu nemi jujjuya ci gaban da INEC ta riga ta rubuta ba a aikace na zamani wajen gudanar da zabe ba.”
Da yake magana kan taken taron, ‘Tsaron Dan Adam da ci Gaban Kasa: Tsari Domin Dukkan Al’umma’, tsohon Shugaban ya ce ya kamata a mai da hankali kan tsaron dan adam.