For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ina Sane Da Irin Wahalar Da ‘Yan Najeriya Ke Ciki – Buhari

Shugaban Kasa Muhammad Buhari a ranar Larabar nan ya bayyana cewa yana sane da irin wahalar rayuwar da ‘yan Najeriya ke ciki wajen ciyar da kansu da kuma iyalansu a zamanin gwamnatinsa.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a hirarsa da gidan Talabijin na Channels, inda ya hori ‘yan Najeriya da su koma gona domin neman mafita.

“Ina sane da ita (wahalar rayuwar da ‘yan Najeriya ke ciki)”, in ji Buhari.

“Amma kamar yanda na ce, kalli yawan al’ummar Najeriya, iya kaso 2.5 cikin dari na kasar noman abinci ake amfani da shi.

“Mun gano hakan ne a makare, amma dai ya kamata mu koma gona”.

KU KARANTA:

A hirar ta Shugaba Buhari ya bayyana irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu daga hawanta kawo wannan lokaci.

“Idan ‘yan Najeriya za su yiwa wannan gwamnati adalci, shine su gane cewa, daga lokacin da muka ci zabe a 2015 kawo yanzu, cikin alkawura uku da mukai – inganta tsaro, habbaka tattalin arziki, da kokarin yaki da cin hanci da rashawa. A fannin tsaro, kasar a bangaren Arewa maso Gabas, idan ka tambayi kowa daga jihar Borno, daga jihar Yobe, daga jihar Adamawa, akwai kananan hukumomi – kusan guda 18 – wadanda suke hannun Boko Haram, yanzu haka babu wata karamar hukumar da ta ke hannun Boko Haram ko ISWAP. Saboda haka, duba da wannan, mun yi wani abu.”

“A bangaren tattalin arziki, kar ka manta, na kalubalanci mutane da yawa da su je su bincika Babban Bankin Najeriya ko NNPC. Fitar da danyen mai daga 1999 zuwa 2014 shine ganga miliyan 2.1 a rana. Amma da muka zo, masu barnata bututun mai sukai ta aikinsu a yankin Kudu maso Kudu.

“Fitar da man ya yiwo kasa zuwa rabin miliyan a rana, sannan kuma farashin man ya fadi zuwa dala 37 duk ganga. Amma duk da haka kalli irin abubuwan da mukai a dan lokacin duk da karancin abubuwan da muke da su idan aka kwatanta da gwamnatin da muka gada.”

Comments
Loading...