Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa, za ta zuba idanuwanta kan ‘yan siyasa da jam’iyyu domin bibiyar hanyoyin samun kudaden yakin neman zabensu a zaben shekarar 2023.
Hukumar za ta kafa kwamitin da zai kula da kashe kudade domin zabe kafin zaben.
Shugaban Hukumar INEC, Mahmood Yakubu, wanda Kwamishinan Kasa na Hukumar, Kunle Ajayi ya wakilta ne ya bayyana hakan ranar Jumuah a Abuja a yayin tattaunawa kan kashe kudade wajen yakin neman zabe.
Kungiyar The Electoral Forum wadda ta samo asali daga Research, Innovation and Advocacy in Development da gudunmawar MacArthur Foundation ne suka shirya tattaunawar.
Shugaban INEC ya bayyana cewa, “Matukar ba mu sanar da kowa ba cewar, tseren neman zaben shekarar 2023 ya fara, to babu ruwanmu da abin da mutum yake yi. Muna bin doka ne yanda ya kamata.
“A hukumance ba mu fitar da sanarwar fara neman Babban Zaben 2023 ba, amma duk lokacin da muka sanar, to za mu sanya kwamitocinmu na lura da al’amura su fara aiki, irinsu Babban Bankin Najeriya, DSS, EFCC, ICPC, bankuna, da sauran masu sanyawa a bi doka. Mun riga mun shiryawa hakan tuntuni.
“Kowanne dan takara dole ne ya bayyana mana yanayin asusun bankinsa. Nan inda suke ciro kudadensu, saboda haka za mu sa su suna gabatar mana da statement of account tun daga farkon lamari.
“Za mu sanya ya zama wajibi a kansu, gabatar da bayanan asusunsu, saboda haka idan suka ce sun yi allon tallen dan takara kuma asusu bai ragu ba, to za mu gane akwai matsala.”
Shugaban INEC ya kuma ce, INEC za ta kuma kula da yawon kudade a ranakun zabe domin dakile siyen kuri’u.
Ya ce, ta hanyar hadinguiwa da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, EFCC, za a sanya bankuna suna gabatar da duk wani abun zargi da suka sansano a hada-hadar kudade domin zabe.
Shugaban na INEC, ya yi barazanar tuhumar duk bankin da ya ki bayar da hadinkai kan hakan.
Da yake karin haske kan mummunar al’adar nan ta siyen kuri’u, Shugaban INEC ya ce, “Za mu kirkiri rundunoni masu duba hada-hadar kudade daga cikin masu zabe wadanda su (‘yan siyasar da jam’iyyu) ba za su san su ba.
“Za mu yi abun ne ta yanda tasirin kudade zai ragu, saboda muna son mu mayar da fagen siyasa, fagen da ‘yan takara masu kudi da ‘yan takara talakawa za su iya fafatawa. Kowa zai kasance a mataki daya, saboda haka ba za ka iya canza tsarin zaben ba.”