Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta ce, hukumar na duba yiwuwar ƙara wa’adin aiki rijistar katin zaɓe da ake gudanarwa.
Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya fada a shafin Twitter na hukumar cewa, hukumar ta ji kiraye-kirayen da ake yi, inda kuma yai alƙawarin cewa, mutane zasu ji daga hukumar kan wa’adin aikin rijistar.
Ya kuma jaddada cewa, mutane zasu sami damar yin rijista, su karɓi katinsu sannan su yi zaɓe, sannan ya ƙara jaddada cewa mutane zasu sami abun da suka zaɓa.
Wannan magana ta Shugaban INEC, ta biyo bayan kiraye-kiraye ne daga gurare da dama na buƙatar hukumar ta ƙara wa’adin aikin rijistar, wanda aka ce zai ƙare a ranar 30 ga watan nan da muke ciki na Yuni.
A jiya Juma’a, Gamayyar Ƙungiyoyi masu Zaman Kansu, sun yi kira ga INEC da ta ƙara wa’adin aikin rijistar.
Gamayyar na ganin cewa, ƴan ƙasa a yanzu, sun ƙara matsa ƙaimi wajen ganin sun sami yin rijistar katin zaɓen, abin da suke ganin ya kamata hukumar ta ƙara musu ƙwarin guiwa ta hanyar ƙara wa’adin aikin rijistar.