For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

INEC Ta Fara Diban Ma’aikatan Zaben 2023

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, a yau Laraba, ta sanar da fara diban ma’aikatan zabe domin tunkarar babban zaben shekarar 2023.

Dalilin hakan, INEC din ta ce, ta bude shafin yanar gizo na diban ma’aikatan, inda tai kira ga wadanda suka cancanta da su fara cikewa.

Hukumar INEC din ta sanar da haka ne a shafinta na Facebook a yau Laraba, inda ta bayyana cewa shafin da aka bude a yau Laraba 7 ga watan Satumba, za a rufe shi ne a ranar 30 ga watan Nuwamba na wannan shekara 2022.

Comments
Loading...