Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, reshen Jihar Katsina ta nuna damuwarta kan karancin fitowar ‘yan jihar domin yin rijistar katin zabe a sabbin akwatina 1,750 da aka samar a jihar.
Kwamishinan Hukumar INEC na Jihar Katsina, Alhaji Jibril Zarewa ne ya baiyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a jiya Juma’a.
Ya ce, shekara guda bayan fara yin rijistar katin zabe, ba a samu fitowar a zo a gani ba a sabbin akwatunan da aka yi a jihar.
Zarewa ya ce, a watan Mayu da ya gabata, kididdiga ta nuna cewa, cikin sabbin akwatuna 1,750 da aka yi a jihar, akwatuna 1,200 ba su sami mutanen da suka kai 50 ba wadanda sukai rijista a kowannesu.
Ya kara da cewa da yawa wasu akwatunan babu ko mutum daya da yai rijista, wasu kuma ba su fi biyar ba, yayinda wasu da aka samu yin, mutanen ba su kai 50 ba.
Ya kuma ce duk da an samu katsewar layikan sadarwa a kananan hukumomi 17 cikin 34 na jihar ta tsawon watanni biyar saboda matsalolin tsaro, tun bayan warwarewar matsalar a watan Maris na wannan shekarar har kawo yanzu cikin akwatina 1,750, akwatina 1,200 ba su da wadanda sukai rijista a cikin kowannesu da suka kai 50.
Kwamishinan INEC din ya kuma yi kira ga wadanda ke yankunan da aka samar da akwatinan da su je su yi rijistar, inda ya bayar da tabbacin cewa INEC a shirye take.
A baya dai Jihar Katsina tana da akwatinan zabe ne guda 4,902 yayin da a yanzu aka kara 1,750 inda a yanzu jihar ke da jimillar akwatina 6,652.