
Manyan lauyoyin da ba su gaza tara ba ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta nada domin su kare sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan February.
Rukunin lauyoyin zai samu jagorancin Tsohon Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Kasa, Abubakar Mahmoud (SAN) yayinda sauran mambobin rukunin suka hada da, Stephen Adehi (SAN), Oluwakemi Pinheiro (SAN), Miannaya Essien (SAN), da kuma Abdullahi Aliyu (SAN).
An samu bayanai daga mamba na rukunin lauyoyi cewa, sauran manyan lauyoyi hudun da ke rukunin, mambobi ne na sashin shari’a na hukumar ta INEC tare kuma da Garba Hassan, Musa Attah da kuma Patricia Obi.
WANI LABARIN: Sabon Shugaban Majalissar Wakilai (Speaker) Zai Fito Daga Jihar Jigawa
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, INEC ta ware zunzurutun kudi naira miliyan dubu uku domin kare sakamakon zaben 25 ga February da zaben 18 ga March na bana.
Da dama cikin wadanda suka fadi a zabubbukan da suka gabata, sun shigar da kara a kotunan sauraron kararrakin zabe suna tuhumar sahihancin zabubbukan.
Tuni dai alkaluma suka nuna cewa, an shigar da kararrakin zabe sama da 100 a duk fadin Najeriya kawo yanzu.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Atiku Abubakar; da na Labour Party, Peter Obi; da na Action Alliance, Solomon Okangbuan; da na Allied Peoples Movement, Chichi Ojei, sun shigar da kararraki suna bukatar da a soke sakamakon zaben shugaban kasa.
A dai ranar 1 ga watan March, 2023 ne INEC ta sanar da Sanata Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 25 ga watan February.