For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Iran Da Saudiya Na Gab Da Maido Da Alakar Diflomasiya

Daga: RFI Hausa

Jakadun Iran sun koma cikin Kungiyar Kasashen  Musulunci mai shalkwata a Saudiya, a wani matakin farko na maido da alaka tsakanin kasashen biyu bayan sun katse huldar diflomasiyarsu a shekarar 2016.

Yanzu haka wakilan Iran sun isa birnin Jeddah na Saudiya domin fara aiki karkashin kungiyar ta  kasashen Musulunci.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiya ta ce, wannan wani mataki ne da ke nuna cewa, kasashen biyu za su mayar da  jami’ansu ofisoshin jakadancin kowanne daga cikinsu.

Kungiyar ta OIC ta ce, tawagar Iran din ta isa birnin Jeddah amma, kawo yanzu babu wani taro da ta halarta, kamar yadda wani jami’i a kungiyar ta Kasashen Musulunci ya shaida wa AFP.

KU KARANTA: An Buɗe Bikin Nuna Fina-Finai Na Duniya A Saudiyya

Sai dai ana sa ran jakadun na Tehran za su halarci wani karamin taron ministoci a ranar 23 ga wannan wata na Janairu  kamar yadda jami’in ya yi karin haske.

Iran wadda ke da yawan mabiya akidar Shi’a da kuma Saudiya wadda ke da yawan mabiya akidar Sunni, dukkaninsu mambobi ne a kungiyar Musuluncin mai kunshe da jumullar kasashe 57.

Kawo yanzu bangarorin biyu da ba-sa-ga-maciji, sun gudanar da jerin tattaunawa har sau hudu a Iraqi tun daga watan Afrilun da ya gabata da zummar maido da alaka a tsakaninsu.

Comments
Loading...