Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce Shugaba Buhari ya yi iya abin da zai iya kan matsalolin da Najeriya ke fama da su, ba kuma zai iya sama da haka ba.
Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya gudana a Abuja kan matsalolin tsaro a ranar Litinin.
Taron ya samu halartar manyan shugabannin addinai da na siyasa da na kabilun Najeriya daga sassa daban-daban.
KU KARANTA WADANNAN:
- Buhari Ya Nada Sabon Minista
- Buhari Ya Bukaci Majalissar Tarayya Ta Karfafa Tsarin Dimokradiyyar Najeriya
- Babu Dan APC Da Zai Bigi Kirji Ya Ce Sun Sauke Nauyin Da Suka Dauka – Danjani Hadejia
Da yake mayar da martani Ministan yaɗa labarai Alhaji Lai Mohammed ya ce ba don zuwan Shugaba Buhari ba da matsalar tsaron Najeriya ta fi haka.
A wani taron manema labarai a Abuja, Lai Mohammed ya ce Buhari ya mayar da batun tsaro a matsayin babban ginshikin gwamnatinsa.
Ya ce magance matsalar tsaro na ɗaya daga cikin abu uku da gwamnatin APC ta fi baiwa fifiko.
Ministan dai na mayar da martani ne ga masu ganin sha’anin tsaro ya ƙara taɓarɓarewa a zamanin gwamnatin APC ta Muhammadu Buhari.