A ranar Asabar 26 ga watan Fabrairu ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta fitar da sabon jadawalin yanda sabgar zaben shekarar 2023 za ta kasance tun daga farko har karshe.
Wannan ya biyo bayan sanya hannun da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kan sabuwar dokar zabe ta shekarar 2022 a ranar Juma’ar da ta gabata.
Jadawalin na INEC ya nuna cewa, za a fara sabgar zaben shekarar 2023 ne daga ranar Litinin 28 ga watan Fabrairu na shekarar 2022 zuwa karfe 12 na daren ranar Alhamis, 11 ga watan Maris na shekarar 2023.
Ga cikakken bayani kan tsare-tsaren.
1. Bayyana Jadawalin Zabe – Litinin 28 ga Fabrairu, 2022.
2. Yin zaben fidda gwanaye, tare da magance matsalolin da suka taso dalilin zaben – Litinin 4 ga Afrilu, 2022 zuwa Juma’a 3 ga watan Yuni, 2022.
3. Cike takardun neman takara ta yanar gizo ga masu neman Shugaban Kasa da gurbin Majalissar Tarayya – Karfe 9 na safiyar Juma’a, 10 ga watan Yuni, 2022 zuwa karfe 6 na yammacin Juma’a, 17 ga watan Yuni, 2022.
4. Cike takardun neman takara ta yanar gizo ga masu neman Gwamna da gurbin Majalissar Jiha – Karfe 9 na safiyar Juma’a, 1 ga watan Yuli, 2022 zuwa karfe 6 na yammacin Juma’a, 15 ga watan Yuli, 2022.
5. Fara yakin neman zaben Shugaban Kasa da ‘Yan Majalissar Tarayya – Laraba 28 ga watan Satumba, 2022.
6. Fara yakin neman zaben Gwamna da ‘Yan Majalissar Jiha – Laraba 12 ga watan Oktoba, 2022.
7. Kare yakin neman zabe ga jam’iyyu na takarar Shugaban Kasa da ‘Yan Majalissar Tarayya – Karfe 12 na daren Alhamis 23 ga watan Fabrairu, 2023.
8. Zaben Shugaban Kasa da na ‘Yan Majalissar Tarayya – Asabar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
9. Kare yakin neman zabe ga jam’iyyu na takarar Gwamna da ‘Yan Majalissar Jiha – Karfe 12 na daren Alhamis 9 ga watan Maris, 2023.
10. Zaben Gwamnoni da na ‘Yan Majalissar Jiha – 11 ga watan Maris, 2023.