Hukumar Shiryar Jarabawar Share Fagen Shiga Manyan Makarantu, JAMB, ta roke Kwamitin Kudi na Majalissar Wakilai da ya ba ta ‘yancin gudanar da kudade ta hanyar cireta daga Ma’aikatu da Sassa a kasafin kudin shekara na Gwamnatin Tarayya.
Wannan na zuwa ne a lokacin da JAMB din ke kuma neman a dawo da tsohon farashin jarabawar na N5,000 wanda a baya aka canza zuwa N3,500.
Rijistaran Hukumar JAMB, Ishaq Oloyede ne ya yi wannan rokon a Abuja a jiya Laraba, a lokacin jin ra’ayin jama’a kan Tsarin Kashe Kudaden Shekara-Shekara na 2023-2025 wanda kwamitin Majalissar Wakilan ya shirya.
Oloyede, ya ce, “Mun gamsu da a ciremu daga cikin kasafin kudi, amma akwai sharuda. Daya daga cikin sharudan shine, misali, lokacin da dalibai sukai rijista a shekarar 2016, mun karbi N5,000 (a kowanne form), kuma haka aka dinga yi a shekaru 5 na bayan (wannan shekara) kafin na shigo JAMB. Lokacin da muka zo, mun sawa gwamnatin naira biliyan 7.5. Mun ji cewa hakan kamar ya yi yawa, sai muka nemi gwamnati da ta rage kudin jarabawar. Amma tun daga nan ba mu kara ko sisin kwabo ba.
“Na yarda cewa, mu mayar da tsohon farashinmu na N5,000 da muke karba a baya.”