Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB, ta sanar da sabbin ranakun rubuta jarabawar ta shekarar 2022.
Dr Fabian Benjamin, Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar ne ya sanar da hakan a mujallar hukumar ta sati-sati.
Hukumar ta sanar da cewa an canza lokacin ne domin a magance wasu matsaloli da suka shafi jarabawar.
Sanarwar ta ce, “A kokarin magance wasu matsaloli, wanda da ma manufar ita ce kara bayar da damar morar shirin ga masu shirin rubuta jarabawar, Hukumar JAMB ta yi wasu gyararraki a jadawalin rubuta jarabawar. Yanzu a sabon jadawalin, Hukumar ta baiyana cewa, za a yi JAMB ta shekarar 2022 a tsakanin Juma’a 6 ga watan Mayu da Litinin 16 ga watan Mayu, 2022.
“Yayin da jarabawar gwaji, MOCK, wadda a baya aka sanya 2 ga Afirilu, 2022, yanzu za a yi ta ranar 16 ga Afirilu, 2022 ga masu sha’awar rubutawa kuma wadanda suka cike form tare da nuna sha’awar yin da wuri.
“Ranar fara yin rijistar jarabawar wadda a baya aka sa cewar za a yi a ranakun 12 ga Fabarairu zuwa 19 ga Maris, tana nan yanda aka tsara.