Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB ta karo maddodi (subjects) 2 cikin maddodin da take da su a baya a matsayin maddodin UTME a bana.
Sabbin maddodin sune: Computer Studies da kuma Physical and Health Education.
Dr. Fabian Benjamin, Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar ne ya bayyana hakan mujallar sati-sati da hukumar take fitarwa.
Sanarwar ta ce, dalibai masu sha’awar rubuta jarabawar, a yanzu za su iya zabar Computer Studies ko Physical Health Education a matsayin wasu daga maddodi 4 da ake rubuta jarabawar a kai, gwargwadon bukatar fannin da za su karanta.
Hukumar ta ce, an kara maddodi biyun ne a ka maddodi 23 da hukumar take da su, yanzu haka sun zama 25 kenan daga shekarar 2022.
Hukumar ta ce, an yi wannan kokarin ne domin a kara fadada damar dalibai a kokarinsu na shiga manyan makarantu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya rawaito cewa kawo yanzu jimillar maddodin da dalibai za su rubuta jarabawar a kai sun kai 25 kenan wadanda suka hada da: Agricultural Science, Arabic, Art, Biology, Chemistry, Christian Religious Studies, Commerce, Economics, French, Geography, Government, Hausa, History da Home Economics.
Sauran sune: Igbo, Islamic Studies, Literature in English, Mathematics, Music, Physics, Principles of Accounts, Use of English, Yoruba, Computer Studies da kuma Physical Health Education.