Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a, JAMB ta kirkiro da guraren yin rijista da kai a Abuja da Lagos ga masu shirin yin rijistar jarabawar JAMB da cike DE a shekarar 2022.
Hukumar JAMB ta ce, tsarin a idan aka gudanar da shi zai kawo raguwar cunkoso a guraren yin rijistar da ake kira CBT Center a biranen.
Tunanin aiwatar da tsarin ya zo ne domin a karfafa guiwar masu son zana jarabawar wadanda suke ganin za su iya yin rijistar da kansu, a kuma fadada damar yin rijistar saboda biyayya ga tsarin kariya daga annobar Korona.
Haka kuma, Hukumar JAMB ta amince da amfani da lambobin 66019 kari bayan 55019 wadda ake amfani da ita tun shekarar 2018 wajen tura sako domin yin rijistar da sauran muhimman abubuwa da suka shafi Hukumar.
JAMB ta ce an yi hakanne domin a samu gudanuwar shirin yin rijistar UTME/DE ta shekarar 2022 cikin nasara, inda za a tabbatar da cewa masu sha’awar rubuta JAMB ko cike DE ba su fuskanci wahala ba wajen kirkirar profile.