Daga: Haruna A Bultuwa
Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB a yau Litinin ta sanar da cewa za a fara rijistar jarabawar JAMB da DE na bana a ranar 12 ga watan Fabarairu, 2022.
Hukumar ta sanar da hakan ne a mujallarta ta sati-sati wadda Daraktan Yada Labaranta, Dr. Fabian Benjamin ya saki kuma TASKAR YANCI ta samu.
A jadawalin tsare-tsaren da suke jikin sanarwar, hukumar ta sanar da cewa, “Za a fara rijistar UTME/DE a ranar 12 ga Fabarairu, 2022 sannan a kare rijistar ranar 19 ga watan Maris, 2022.
Za a yi jarabawar gwaji (Mock) a ranar 20 ga watan Afirilu, sannan a yi jarabawar JAMB a tsakanin 20 zuwa 30 ga watan Afirilu, 2022.