For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

JAMB Zata Ci Gaba Da Tantance Sakamakon Jarabawa 27,105

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a, JAMB ta ce zata ci gaba da tantance jarabawa 27,105 ta wasu dalibai da suka rubuta jarabawar a wannan shekarar ta 2022.

Hukumar ta baiyana hakan ne a yau Litinin a Abuja.

An baiyana wannan kididdigar ne a Mujallar Mako-mako ta hukumar wadda ake fitarwa daga ofishin Shugaban Hukumar.

JAMB din ta baiyana cewa, masu son rubuta jarabawar su 1,761,338 suka yi rijistar rubuta jarabawa.

Ta kuma kara da cewa, mutane 1,707,626 suka zauna rubuta jarabawar, yayin da sakamakon mutane 1,671,203 ya fito.

Ta kuma baiyana cewa an rike sakamakon mutane 69 da kuma ake sake tantance sakamakon mutane 27,105, sai kuma mutane 1,783 da suka sami matsalar daukar hoton yatsunsu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya rawaito cewa, JAMB ta shekarar 2022 an yi ta a ne a tsakanin ranar Juma’a, 6 ga watan Mayu zuwa ranar Juma’a, 13 ga watan na Mayu.

A wani ci gaban kuma, JAMB ta baiyana cewa, ta gudanar da jarabawar ga dalibai ƴan ƙasashen waje a ranar Asabar da ta gabata.

Hukumar ta ce jarabawar ta gudana ne a santocinta guda 5 cikin guda santocin 9 da hukumar ke da su a ƙasashen wajen, kuma an samu nasarar shirin.

JAMB ta ce santocin da aka gudanar da jarabawar sune na Accra, Ghana; Johannesburg, South Africa; Buea, Cameroun, Abidjan, Cote d’Ivoire da Cotonou, Benin Republic.

Ta kuma ce, nan gaba zata gudanar da jarabawar a Berlin, Germany; London, UK, Jeddah, Saudi Arabia da New York na Amurka.

NAN

Comments
Loading...